Gwamna Raɗɗa ya yi ta’aziyar rasuwar Talban Katsina, Jakada Zakari Ibrahim

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamna Dikko Umar Raɗɗa na Jihar Katsina ya nuna kaɗuwarsa bisa rasuwar Talban Katsina, Jakada Zakari Ibrahim.

A acikin wata takarda, Sakataren yaɗa labaran gwamnan Kaula Muhammad, Raɗɗa Ya bayyana marigayi Jakada Zakari Ibrahim a matsayin mai kishin jiharsa da taimakon al’umma, wanda ya riƙe mukamai daban-daban a mataki ba ƙasa.

“Marigayi ya riƙe muƙamin mai kula da tsaro na cikin gida NIA da mataimakin mai bada shawara kan harkokin tsaro na ƙasa da kuma karamin minista a ma’aikatar harkokin waje.”

Dikko Radda ya ce lalle mutuwar Talban Katsina ba karamin rashi bane ga al’ummar Katsina da ma ƙasa baki ɗaya.

Haka kuma marigayin ya kasance mai sadaukarwa wajen aiki tuƙuru a matakin gwamnati da taka rawa a harkokin ɗaukaka jihar a mataki na ƙasa”, inji Raɗɗa.

Gwamnan ya kuma bayyana ƙoƙarin da marigayin ya yi na ɗaukaka darajar masarautun jihar da ƙarfafa alaƙa tsakanin su da gwamnati.

Malam Raɗɗa ya miƙa ta’aziyarsa ga iyalan mamacin da masarautun Katsina da yi masa addu’ar Allah Ya sanya Aljannar fiddausi ta zama makomarsa.

By Babaji