Gwamna Lawal ya rantsar da sabbin shugabannin ƙananan hukumomi a Zamfara

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Gwamna Dauda Lawal ya rantsar da sabbin shugabannin ƙananan hukumomi guda 14 a jihar Zamfara tare da jan hankali kan muhimmancin adalci da daidaito wajen ayyukan ci gaba. A yayin bikin rantsarwar da aka gudanar a ɗakin taro na tsohon majalisar gwamnatin jihar, Gwamna Lawal ya yi kira ga sabbin shugabannin da su fifita jin daɗin al’umma tare da tabbatar da kowa ya ci gajiyar ayyukan ci gaba a yankunansu.

Gwamnan ya yabawa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Zamfara (ZASIEC) saboda shirya zaɓe mai inganci da gaskiya wanda ya bai wa ’yan takarar jam’iyyar PDP nasarar lashe dukkanin kujerun shugabanci a ƙananan hukumomi 14 na jihar. Ya bayyana cewa tsarin ƙananan hukumomi a Najeriya yana da muhimmanci wajen kusantar da gwamnati ga jama’a a matakin ƙasa.

A cikin jawabinsa, Gwamna Lawal ya buƙaci shugabannin kananan hukumomin su haɗa kai da gwamnatin jiha domin samar da cigaba a matakin tushe. Ya kuma yi nuni da cewa akwai shirye-shiryen zuba jari da gwamnati ta ƙirƙiro domin samar wa matasa ayyukan yi da kuma rage yawan aikata laifuffuka. Gwamnan ya ja hankalinsu da su rungumi gaskiya da adalci wajen tafiyar da dukiyar jama’a.

Haka kuma, Gwamna Lawal ya yi kira ga sabbin shugabannin da su shiga cikin al’ummominsu sosai domin jin matsalolin su da kuma tabbatar da cewa kowa ya samu wakilci nagari. Ya buƙace su da su kula da raunana masu buƙatu na musamman kamar mata, yara, nakasassu da tsofaffi a cikin ayyukansu. Gwamnan ya jaddada buƙatar su zama abokan tafiya ga gwamnatin jiha wajen aiwatar da shirye-shirye a ɓangarorin tsaro, ilimi, noma, ci gaban tattalin arziki, lafiya da kuma ci gaban ababen more rayuwa.

A ƙarshe, Gwamnan ya ja hankalinsu da su riƙa ajiye bayanan kuɗaɗen da suke kashewa tare da duba su lokaci-lokaci domin tabbatar da gaskiya da ingancin mulkinsu.

By ukarofi