Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kamfanin talbijin na Multichoice, mai kula da gidan talbijin na Pay-Tv na Afirka ta Kudu, ya bayyana cewa sashinta na Nijeriya, ya yi rasa kwastamomi masu biya kuɗi don si kallo sama da 243,000 a DSTV da GOtv a cikin watanni shida na Afrilu zuwa Satumba na wannan shekara.
Kamfanin ya bayyana hakan ne a cikin Sakamako na Kuɗi na wucin gadi na watanni shida da suka ƙare a ranar 30 ga Satumba, 2024, wanda aka fitar ranar Talata.
A cewar kamfanin, hauhawar farashin kayayyaki a Nujeriya sama da kashi 30 cikin 100 sakamakon tsadar kayan abinci da wutar lantarki da kuma man fetur ya tilasta wa da yawa daga cikin abokan hulɗar sa yin watsi da na’urorin nasu.
A cikin rahotonsa na kuɗi na Maris 2024, MultiChoice ya bayar da rahoton asarar kashi 18 na masu biyan kuɗi a Nijeriya.
Kamfanin ya kuma bayar da rahoton asarar masu rajista 566,000 a sauran ayyukan Afirka a cikin watanni shida da suka gabata, inda Zambia da Nijeriya suka ba da gudummawa mafi girma ga wannan raguwar.
“Tare da sauran kasuwancin Afirka da aka samu raguwar masu biyan kuɗi 803k a cikin 2H FY24, wannan raguwar ya ragu zuwa 566k a cikin 1H FY25,” in ji MultiChoice.
Asarar ta haɗa da 298,000 a Zambiya da 243,000 a Nijeriya, yayin da sauran kasuwannin suka samu raguwar kaɗan.
Matsanancin hauhawar farashin kayayyaki da rashin kwanciyar hankali na kuɗi sun yi mummunar tasiri ga ribar kamfanin, tare da Babban Jami’in Kamfanin MultiChoice Calvo Mawela ya yi tsokaci, “Muna samun ci gaba mai kyau wajen magance matsalar rashin fasaha wanda ya haifar da shigarwar lissafin kuɗi ba tare da tsabar kuɗi ba a ƙarshen shekara.”
Mawela ya bayyana cewa ana sa ran matsayin kamfanin zai farfaɗo daga watan Nuwamba.
