An yi walimar matan aure 10 da suka haddace Alƙur’ani a Argungu

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi

An gudanar da walimar bikin walimar matan aure goma da suka haddace Alƙur’ani maigirma a makarantar Kulliyatu Abubakar Majidadi Al-Islamiyya Gidan Tafida da ke garin Argungu.

Malam Nasiru Abubakar Mera shi ne shugaban makarantar kuma ya zanta da wakilinmu jim kaɗan bayan kammala walimar ranar Lahadin da ta gabata inda ya bayyana jin daɗinsa da godiyar Allah da ya nuna musu wannan ranar da suka daɗe suna jira.

Ya ce mata goma sha ɗaya ne suka haddace Alƙur’ani maigirma sai dai ɗayar mai suna Hauwa’u Ahmed Musa Gulma ta riga ta yi aure kuma tana Zamfara saboda yanayin matsalar tsaro ba ta samu zuwa ba amma dai Alhamdu lillah.

“Ba shakka wannan ba ƙaramar nasara ba ce aka samu tun kama daga Sanata Umar Abubakar Tafida mataimakin gwamna, wanda shi ne ya gina makarantar zuwa malamai da su kansu. ɗalibai zuwa mazajensu da suka ba su ƙwarin gwiwa da isashshen lokaci don ganin sun cimma wannan burin na su, saboda haka muna addu’ar Allah ya sakawa kowa da mafificin alkhairi.

“Yanzu haka akwai mata da yawa da suka daina zuwa makaranta amma saboda ganin wannan cigaba da aka samu ya sanya sun dawo.

“Dalilin da ya sanya aka buɗe wannan sashen na haddar Alƙur’ani maigirma shine lura da taɓarɓarewar karatun mats ne bayan sun yi aure, saboda sai da yawa za ka ga mace ko da tana da hizifi goma ko ma fiye da hakan da zarar ta yo aure sai ka ya ta zubar da su saboda haka ya sanya muka ya ya kamata su ci dage su cigaba. Aƙalla akwai waɗanda suka haddace Alƙur’ani maigirma cikin shekaru bakwai wadansu goma wadansu sha biyu zuwa Sha biyar amma dai yau shekaru goma sha shida ne da soma wannan karatun na hardar Alƙur’ani.

Ya yi kira ga masu hannu da shuni da su yi koyi da Mataimakin gwamna Sanata Umar Abubakar Tafida saboda bayan gina makarantar yana kuma ɗaukar nauyin waɗansu al’amurra na yau da kullum.

Bayan wannan ya sadaukarda wannan makarantar wanda ya ke nuna yana daga cikin mutanen da Allah ya ambata da Waladun salihu a cikin Alƙur’ani, waɗanda ke aikawa iyayensu lada a cikin kaburransu.

Tun farko da ta ke jawabi a madadin Hajiya Zainab Nasir Idris Uwargidan gwamnan Kebbi, babbar Sakatariya a ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu Hajiya A’isha Muhammadu Maikurata ta ce uwargidan gwamnan Kebbi ta bayarda kyautar naira milliyan daya ga wadannan matan tare da jinjina musu da kuma fatar Allah ya sa wannan karatun ya zamo mai amfani garemu bakidaya ya zamo sanadiyyar shiga Aljanna.

Ta yi kira ga wadanda ke da hali da su Gina makarantu musamman na addinin musulunci don koyar da mata da yara don ganin an sami tsarkakakkiyar al’umma inda ta jaddada kudurinta na bayar da gudummawa ga wannan makarantar don ganin an inganta karatun matan aure.

Taron dai ya samu halartar Hajiya Zainab Tanko Sununu, matar Ministan Jinƙai da Agaji da sauran ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa da kuma malaman addini.

By ukarofi