
Daga UMAR GARBA a Katsina
Wata mai yi wa qasa hidima ta NYSC mai suna Nafisa Umar Hassan, ta bayar da tallafin kayan makaranta ga ɗalibai 100 a makarantar firamare ta ƙaramar hukumar Ɓatagarawa da ke Jihar Katsina.
Nafisah mai lamba KT/24A/1178 wadda a halin yanzu ke gudanar da aikin hidimar a Ma’aikatar Muhalli ta jihar, ta raba kayan makarantar ne ga ɗaliban a harabar makarantar.
Da take jawabi ga waɗanda suka ci gajiyar tallafin, Nafisa ta ce hakan yana daga cikin tallafi da ƙungiyarta ta tallafawa al’umma ke bayarwa da nufin rage raɗaɗin halin da iyayen yaran ke ciki gami da tallafa wa iliminsu.
Ta kuma bayyana cewa waɗanda suka ci gajiyar tallafin ɗalibai ne da suka fito daga gidajen talakawa waɗanda iyayensu ba sa iya sayen kayan karatu da kuma waɗanda suka rasa iyayensu sakamakon munanan ayyukan ƴan bindiga.
“Na soma wannan aikin ne don in taimaka wa ɗaliban domin yawancinsu suna da sha’awar zuwa makaranta kuma suna da ƙwazo. Hakan zai taimaka musu wajen neman ilimin firamare”, inji ta.
A nasa jawabin, Kodinetan hukumar NYSC a jihar, Ibrahim Saidu, ya godiya ga ƴar hidimar ƙasar bisa tallafin da ta bayar.
Ya yi kira ga sauran masu yi wa ƙasa hidima a jihar da su yi koyi da ita ta hanyar gudanar da makamantan ayyyuka irin haka don taimakon al’umma.
Daga nan ne ya kuma buƙaci shugabannin ƙananan hukumomi 34 na jihar da su riƙa bai wa masu yi wa ƙasa hidima goyon bayan da suke buƙata domin gudanar da ayyukansu na ci-gaban al’umma cikin walwala.
