Tsagaita wuta kan Lebanon ba cinya ba ƙafar baya

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Afkuwar muhimman lamura a gabar ta tsakiyar kan yaƙin da Isra’ila ke yi da Hamas da ya shafi Hezbollah da Houthi ya sa har ila yau za mu sake duba yadda lamuran su ke don haskawa kan fahimtar gaskiya. Shin tsagaita wuta kan Lebanon zai kawo maslaha ko samar da bakin zare ko dai za a cigaba da ganin hayaƙi bayan labarun kashe harshen wuta. Duk wannan zai zama abun sa ido a duniya. 

Makon jiya mun yi magana kan hukuncin kotun duniya da kuma ba a ga wata kasa ta dau mataki kan Isra’ila ba. Za mu tuna yadda daga nan Afurka ma ƙasar Afurka ta kudu ta shigar da kara don a tuhumar Isra’ila da kisan kare dangi kan Falasdinawa. Kotun ta goyi bayan matsayar Afurka ta kudu amma sam hakan bai canja komai a kan Isra’ila ba. Maimakon hakan ma har shagube da neman shashantar da hukuncin Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi. 

Kwatsam sai ga sabon umurnin kotun na a cafke Netanyahu a mika ma ta shi don ya fuskanci hukuncin laifukan yaƙi a Gaza. Baya ga Netanyahu kotun na neman tsohon ministan sa na tsaro Yoaɓ Gallant da kwanan nan Netanyahun ya kwabe shi don shi ma a cafke shi ya fuskanci irin wannan tuhumar. 

Kotun ta duniya ba ta tsaya kan jami’an nan na siyasar Isra’ila ba ta kuma ce a kamo ma ta jagoran soja na Hamas Muhammad Deif wanda za ta tuhuma da laifin kai farmaki cikin Isra’ila ranar 7 ga watan Oktobar bara. 

An ba da labarin kashe Deif amma ba shaidar hakan tun da ga shi ita kan ta kotu ta na neman sa. Kazalika kotun ta ce mutum 3 ne ta ke nema a cikin Falasɗinawa amma biyu sun riga mu gidan gaskiya. A fahimtar gaggawa akwai tsoffin shugabannin Hamas biyu Isma’ila Haniyeh da Yahaya Sinwar. A nan mun ga kenan duk wani hukuncin da kotun duniya za ta iya wanda ta ke zargi ba zai fi kisa ko ɗaurin rai da rai ba irin yanda mu ka ga ya auku ga tsohon shugaban Laberiya Charles Taylor. 

Yanzu tun da Isra’ila ta kashe mutum biyu da kotun ke nema a Hamas shikenan magana ta kare sai dai ko a aiyana hukuncin da za a iya yi mu su da su na raye. Tuni ofishin Firaministan Isra’ila y ace zai ƙalubalanci hukuncin ko ɗaukaka ƙara don sake bitar lamarin ya kai ga an janye umurnin cafke Netanyahun. Wani abun dubawa ma shi ne Isra’ila inda Netanyahu ya ke abun da ya ga dama ba sa cikin membobin kotun hakanan ma Amurka da ya kan ziyarta. Don haka zai iya yawo ko ina a ƙasashen biyu ba mai ce ma sa kanzil. 

Manyan ƙasashen duniya da musamman na yamma kan iya daurewa hukuncin kotun baya a kuma samu nasara. In an duba yadda a ka takura tsohon shugaban Sudan Omar Elbashir da ma barazanar za a iya cafke shugaban Rasha ɓladimir Putin. Hukuncin kotun na buƙatar ƙasashe masu fada a ji su mara baya kafin hakan ya yi nasara ko da kuwa Majalisar ɗinkin Duniya za ta ɗau matsaya mai tsauri.

Isra’ila ta sanar da cimma yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta kan Hezbollah a Lebanon bayan wata 4 na fitina.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya gabatar da ƙudurin da majalisar sa ta amince da shi amma hakan ba zai hana kai farmaki ba in buƙata ta taso.

Har jawabi Netanyahu ya gabatar kan dakatar da yaƙin da ya nuna hakan zai sa Isra’ila ta mayar da hankali kan Iran da killace Hamas a Gaza.

Wani abun mamaki ma hatta bayan ayyana yarjejeniyar sai da Isra’ila ta kai mummunan farmakin jiragin yaƙi da ya girgiza babban birnin Lebanon, Beirut.

Hezbollah da gwamnatin Lebanon sun ce batun Isra’ila za ta iya kai farmaki a lokacin da ta g a dama bay a cikin yarjejeniyar.

Hakanan wani harin Isra’ila daf da cimma yarjejeniyar ya yi sanadiyyar mutuwarkimanin mutum 42 a Lebanon.

Ba alamar wannan yarjejeniya za ta dakatar da hare-haren kisa kan Gaza da su ka faro tsawon watanni 14 da su ka wuce.

Amurka da Faransa su ka jagoranci ƙulla wannan yarjejeniya, inda shugaba Joe Biden na Amurka ke cewa Amurka yanzu za ta kawo sabuwar hanyar tsagaita wuta a Gaza.

Yarjejeniyar na nuna Isra’ila za ta janye sojojin ta daga kudancin Lebanon inda sojojin gwamnatin Lebanon za su maye gurbin su.

Firaministan Lebanon Najib Mikati ya yi maraba da yarjejeniyar da Amurka ce kan gaba wajen ƙulla ta.

Sabon shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump ya yi alwashin zai kawo ƙarshen fitinar ta gabar ta tsakiya duk da bai fayyace dabarar da zai bi ba.

A 2020 lokacin Donald Trump ya na fadar White House ya dau matakan ƙulla yarjejeniyar sanya ƙasashen Larabawa su ƙulla dangantaka mai ƙarfi ta diflomasiyya da Isra’ila bisa tarihin ‘yan uwantaka daga Annabi Ibrahim. Wato yarjejeniyar ta ABRAHAM mun yi magana a kan ta inda manyan ƙasashen Larabawa in ka deɓe Saudiyya da ke da sharadi su ka gana da Trump a Washington ya sanya su rantaba hannu tare da Netanyahu kan yarjejeniyar. A lokacin shi kan sa shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas daga fadar sa a Ramallah ya nuna matukar takaicin hakan da zaiyyana yarjejeniyar da cewa ‘yan uwan su Larabawa sun ci amanar su. 

Wannan a lokacin bai hana kasashen karfafa huldar su da Isra’ila ba. Shugaban Turkiyya Raceb Erdoan duk da ba Balarabe ba ne ya marawa Falasdinawa baya da watsi da yarjejeniyar. Hakika in ba don Erdoan ya kama kasa ba da matsayar sa ta sa shi ma yau ya zama tarihi. Duk da nuna kamar hakan wata nasara ce, Trump kuma ya dau wani mataki na amincewa da aiyana birnin Kudus a Falasɗinawa a matsayin babban birnin Isra’ila. 

Wato har ma Amurka ta dau matsayar kaurar da ofishin jakadancin ta daga birnin Tel’Aɓiɓ zuwa ƙudus. Babbar fata a nan in Trump ya fara sabon wa’adi ya ɗau matakan dakatar da wannan fitina gaba ɗaya ba a Lebanon kaɗai ba. Kazalika a samu kafa ƙasar Falsɗinu mai ‘yanci.

Sabbin labarun fitinar gabar ta tsakiya:

Saudiyya na ƙarfafa batun samun salama a gabar ta tsakiya a wajen taron ƙungiyar ƙasashe 7 masu ƙarfin tattalin arziki G7 da kuma ƙasashen Larabawa.

Taron dai wanda ya gudana a Italiya ya samu halartar Saudiyya, katar, Jodan, Daular Larabawa da Masar.

Ministan wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan ya ɗauko batun yakin da a ke yi a Gaza da Lebanon da ya ce ya dace a tsayar da shi nan take.

Kazalika, bin Farhan ya buƙaci a ɗau matakan kafa ƙasar Falasɗinawa mai zaman kan ta da ke cikin tsoffin hanyoyin da a ke kawowa na samun maslaha.

Firaministan Lebanon Najib Mikati ya ce harin da Isra’ila ta kai kan cibiyar sojan Lebanon na nuna yin biris da neman tsagaita wuta.

Wannan na zuwa ne bayan ziyarar da wakilin ƙungiyar taraiyar turai Joseph Borrell ya kawo babban birnin Lebanon Beirut ya na mai kiran tsagaita yaƙi tsakanin Isra’ila da Hezbollah nan take.

Mikati ya ce wannan zubar da jini da Isra’ila ke yi sako ne na ba ta son tsagaita wuta don haka ya dace ƙasashen duniya su dau matakin da ya dace.

Harin dai ya yi sanadiyyar mutuwar sojan Lebanon daya inda guda sha takwas kuma su ka samu raunuka.

Hezbollah a na ta ɓangaren ta ce ta cilla rokoki cikin Isra’ila inda kuma su ka dira a inda a ke buƙata.

An ga gobara ta kama a tsakiyar Isra’ila inda majiyar Isra’ila ta ce Hezbollah ta cilla ma ta rokoki 160.

Isra’ila ta kai munanan hare-hare a kudancin Lebanon da waje da babban birnin ƙasar Beirut.

A sanadiyyar hare-haren kimanin jami’an kiwon lafiya biyar su ka rasa ran su kuma babu ma labarin waɗanda su ka samu raunuka.

Sojojin ƙasa na Isra’ila kuma na cigaba da samun turjiya daga ‘yan Hezbollah a kudancin na Lebanon.

Haƙiƙa hare-haren nan na Isra’ila na kawo tarnaki ko ma rashin fata ta tsagaita wuta bisa alwashin wakilin Amurka Amos Holstein duk da dai a karkace an aiyana tsagaita wuta

Wakilin dai in za a tuna ya sauka a Beirut inda ya nuna a na daf da samun sulhun tsagaita wuta; inda hakan ya tabbata amma da rakiyar miyagun hare-hare daga Isra’ila.

Holstein ma ya shiga Isra’ila inda ya gana da Firaminista Netanyahu kafin ya koma Washington.

Da alamun Isra’ila ba ta da niyyar daina kai farmaki kan Hamas a Gaza da kuma Hezbollah a Lebanon.

Zuwa yanzu hare-haren na Isra’ila sun yi sanadiyyar kashe ‘yan Lebanon kimanin 3, 800 da kuma hakan bai haɗa da ‘yan Hezbollah da su ka rasa ran su a fagen daga ba.

Kammalawa;

Yaushe za a daina kashe mata da ƙananan yara a Gaza? Haƙiƙa yaƙin nan ba zai gushe a ƙanƙanin loakci ba ko da yau ɗin nan a ka daina kai hare-hare. An tabbatar da zaman gawawwaki a ƙarƙashin gine-gine da jiragen yaƙin Isra’ila su ka ruguza a Gaza. Sauran mutane da ke da rabon shan ruwa ka iya komawa su fara sabuwar rayuwa a gurbin gidajen su a Gaza da cigaba da jajantawa juna har ranar da wani sabon lamari mai daɗi ko marar daɗi ya baiyana.

By ukarofi