Ta yaya za ki kula da fatarki a lokacin sanyi

Daga AISHA ASAS 

Yayin da aka ce sanyi ya ƙarato, mutane da yawa suna tausayawa halin da fatarsu za ta shiga yayin da suka yi arangama da yanayin na sanyi.

A lokacin sanyi fata na yamushewa saboda yanayin iskar hunturu, kuma yakan yi muni musamman ga waɗanda ba su san yadda za su ba wa fatar tallafi ba.

Yanayin sanyi ba iya fata ya tsaya ba, domin hunturu na taɓa lafiyar gashi, ta hanyar yawan karyewa, sai kuma uwa uba kaushi ko fasau da ƙafa ke yi.

Waɗannan matsalolin na lokacin sanyi na sauya fasalin jiki tare da sanya shi damuwa, har ta kai kwalliya ma ba ta cika fita raɗau yadda ake so ba a lokutan sanyi.

Matakan da ya kamata ki ɗauka a lokacin sanyi:

A guje wanka da ruwa masu zafi: na san mai karatu zai iya cewa hakan ba mai yiwa ba ne, kasancewar ya zama al’ada da muke yi a duk lokacin da aka ce sanyi ya yi sallama. Sai dai abinda ba ku sani ba shi ne, wanka da ruwan zafi na ɗaya daga cikin ababe masu bayar da gudunmuwa ga lalacewar fata. Don haka idan ya zama dole amfani da ruwan zafi, to a yi da masu ɗumi.

Yawaita shafa mai: idan muka kalli yanayin yadda lokacin hunturu yake kasancewa na daga iska da ke saurin busar da jiki da kuma sanyin wanda ke dasƙare abokanin tafiyar fatar, za mu ga cewa, kusan kodayaushe fatar tana ƙoƙarin bushewa ne, hakan ke sa irin shafar da ka ke yi masa a baya ba zai wadatar ba. Don haka yake da muhimmanci yawaita shafawa fatar mai. Kuma idan za a haɗa man shafawa na lokacin sanyi, yana da kyau a haɗa shi da mai ruwa-ruwa, wato lotion, saboda yana taimakawa fata wurin jiƙa ta.

Yawaita shan ruwa: a lokacin sanyi, buƙatuwar mu da ruwa kan ragu sosai ta yadda za ka iya ɗaukar tsayin lokaci ba tare da ka ji buƙatar ruwa ba, don haka muke kauce wa shan su, sai dai abinda ba mu sani ba shi ne, bincike ya tabbatar da cewa, fata na matuƙar buƙatar ruwa a lokacin sanyi, don hana ta yawan bushewa da kuma ƙara mata inganci, don haka rashin isasun ruwa a jiki na ɗaya daga cikin ababen da ke taimako wurin bushewar fata a lokacin sanyi.

Gyaran jiki: akwai gyaran jiki da mata ke yi musamman lokacin da za su iya aure, don ƙara wa jikinsu kyau, sai dai wasu daga cikinsu na hawa layin abubuwan da ke kawowa fata agaji a lokacin sanyi, kamar dilka da halawa. Yana da kyau mata su sanya irin wannan gyaran jiki a layin ababen da suke yi a lokutan sanyi, don ganin fatarsu ba ta shiga mawuyacin hali ba.