An yi asarar biliyoyi bayan gobara ta kama rumbun Hukumar Tallafa Wa Al’umma Ta Ƙasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Wata gobara da ta kama a rumbun Hukumar Tallafa Wa Al’umma Ta Ƙasa (NSIPA) dake yankin Idu a Abuja, ta yi sanadiyyar asarar wasu kayayyaki na biliyoyin nairori.

Kayayyakin an samar da su ne don gudanar da horo ga masu cin gajiyar shirin N-power.

A game da faruwar lamarin, ƙaramin Ministan Jin-ƙai da Taƙaita Talauci, Dakta Yusuf Sununu ya samar da kwamitin mutane biyar da za su yi bincike a kai.

A yayin ziyararsa wajen da al’amarin ya auku, Ministan ya bada tabbacin cewa za su ɗauki matakan kariya don kaucewa sake faruwar irin haka a nan gaba.

A cikin wata takarda da Daraktan Labaran Ma’aikatar, Rhoda Ishaku ya fitar, Sununu ya bai wa kwamitin wa’adin mako biyu don su bayar da rahoton binciken nasu.

Ministan ya kuma yaba wa Hukumomin Kula da Gobara a mataki na ƙasa da na birnin tarayya Abuja da kuma kamfanin Julius Berger a ƙoƙarinsu na tabbatar da kashe wutar.

By Babaji