Ba a janye ƙudirin dokar haraji ba – Akpabio

Spread the love

Majalisa za ta bi matakan doka babu tsoro, inji shi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Majalisar Dattijai ta Nijeriya ta jaddada aniyarta ta ci gaba da bin tsari daki-daki wajen aiwatar da ƙudirin gyaran haraji, inda ta ce, babu wani ɓangare na aikin da aka dakatar ko janye shi.

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana a zaman majalisar a ranar Alhamis cewa majalisar ta ci gaba da mayar da hankali kan aikinta na wakiltar muradun ‘yan Nijeriya kuma ba za ta tsorata da matsin lamba daga waje ba.

Dangane da batun umarni da shugaban majalisar dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, Akpabio ya yi watsi da rahotannin da kafafen yaɗa labarai ke yaɗawa na cewa an dakatar da tattaunawa kan ƙudirorin.

Da yake watsi da duk wani yunƙuri na matsin lamba a zauren majalisar, shugaban majalisar ya kuma bayyana cewa, “Ba za a iya cin zarafin majalisar ba. Duk wani garambawul da muka gamsu zai biya buƙatun ‘yan Nijeriya. Waɗannan ƙudirorin sun ƙunshi tanade-tanade waɗanda za su amfanar da jama’a.”

Shugaban Majalisar Dattawa a cikin jawabinsa, ya kuma yi gargaɗin a guji yaɗa labaran ƙarya da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta ko kafafen yaɗa labarai, inda ya buƙaci jama’a su mai da hankali ga faɗan gaskiya.

“Ba mu dakatar ko janye shawarwarin da aka yi na gyaran haraji ba. Duk wani yunƙuri na tsoratar da majalisar dattawan bai dace ba. Wannan ƙudiri ne na majalisar zartarwa, kuma sashin zartarwa ne kawai zai iya janye su. Mun ci gaba da tsayawa tsayin daka a kan ayyukanmu na majalisa.”

Ya kuma ƙara jaddada ‘yancin kan majalisar, yana mai cewa, “Ba ma karɓar umarni daga kowa ko wani ofishi, komai girman matsayi.”

Sanata Akpabio ya jaddada cewa majalisar dattawan ba ta gaggawa kuma za ta yi cikakken aiki a kan ƙudirorin da ke gaban majalisar don haka ta ƙara ɗaukar matakan yin doka kan ƙudirorin, ciki har da kafa wani kwamiti na musamman da ke wakiltar shiyyoyi shida na siyasa a Nijeriya don yin aiki da majalisar. Babban Lauyan Tarayya (AGF), Lateef Fagbemi, don magance batutuwan da ke haifar da cece-kuce.

Shugaban majalisar dattawan ya bayyana cewa taron jin ra’ayin jama’a da tuntuɓar masu ruwa da tsaki da suka haɗa da gwamnoni da malaman addini da ‘yan kasuwa ya zama wajibi a warware duk wani rashin tabbas.

“Idan makonni shida ba su isa ba, za mu tsawaita lokacin. Mun himmatu wajen tabbatar da gaskiya da magance duk wata damuwa,” inji shi.

A ranar Laraba ne Majalisar Dattawa ta kafa wani kwamiti da zai yi nazari a kan ƙudurorin dokar  haraji da ke gaban Majalisar Dokokin ƙasar.

A cewar mataimakin shugaban majalisar dattawa, Jibrin Barau, wanda ya jagoranci zaman majalisar a ranar Laraba, kwamitin da ke ƙarƙashin jagorancin shugaban marasa rinjaye, Sanata Abba Moro (PDP, Benue ta Kudu) zai gana da babban lauyan gwamnatin tarayya, Lateef Fagbemi, don yin magana a wuraren da ke cikin ƙudurorin da kuma komawa Majalisar Dattawa kafin sauraron jama’a.

Barau ya lura cewa ɓangaren zartarwa na gwamnati ya amince da majalisar dattawan cewa akwai buƙatar a warware dukkan matsalolin da ke haifar da saɓani a cikin ƙudirorin.

Tun lokacin da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya miƙawa majalisar dokokin ƙasar wasu ƙudirori guda huɗu na gyara dokar haraji a watan Oktoba, ta fuskanci turjiya musamman daga yankin Arewacin ƙasar nan.

By ukarofi