Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da korar wasu ma’aikatan Gwamnatin Tarayya da suke da digiri daga manyan jami’o’i masu zaman kansu a Jamhuriyar Benin da Togo.
Umarnin hakan ya shafi ma’aikatan tarayya da suka kammala karatunsu a makarantun tun daga shekarar 2017 zuwa yanzu.
Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Segun Imohiosen, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a ranar Laraba.
A cikin watan Agusta, Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa jami’o’i takwas ne kawai aka amince da su don ba ‘yan Nijeriya digiri a Togo da Jamhuriyar Benin.
Hakan ya biyo bayan wani rahoton sirri da wani ɗan jaridar Daily Nigerian ya yi bayan ya samu digiri a wata jami’a a jamhuriyar Benin cikin watanni biyu ya kuma yi amfani da shi wajen shiga shirin yi wa ƙasa hidima ta NYSC.
Bayan rahoton, gwamnati ta haramta amincewa da takardar digiri na manyan makarantu a Jamhuriyar Benin da Togo.
Gwamnatin tarayya ta kuma kafa wani kwamitin bincike na ma’aikatun kan masu takardar shaidar karatun digiri don bincikar ayyukansu.
Ministan Ilimi na lokacin Tahir Mamman ya bayyana cewa sama da ‘yan Nijeriya 22,500 ne suka samu takardar shaidar digiri na bogi daga jamhuriyar Benin da Togo kuma za a soke irin waɗannan takardun.
Mamman ya bayyana cewa hakan na daga cikin rahoton da kwamitin binciken da aka kafa domin binciken badaƙalar shaidar digiri na jami’o’in ƙƙsashen waje da na cikin gida a Nijeriya ya miƙa wa majalisar zartaswar tarayya.
