Za mu dawo kan ganiyarmu idan ’yan wasanmu suka murmure – Guardiola

Spread the love

Kocin Manchester City, Pep Guardiola, ya ce za su sake dawowa ganiyarsu idan har duka ‘yan wasansa suka kammala murmurewa.

Da dama daga cikin ’yan wasan ƙungiyar na Man City sun sha fama da rauni, musamman zakarar kyautar Ballon d’Or Rodri da Kyle Walker da Jack Grealish da Kevin De Bruyne da Mateo Kovacic sai kuma Ruben Dias.

Wannan rauni ya sanya Man City ta samu mummunar koma baya a wannan kaka, musamman ma yadda ta yi kunnen doki daya a cikin wasanni 7 na baya-bayan da ta yi a dukkanin gasannin da take fafatawa, sannan ta yi rashin nasara a 6.

Zakarar gasar Firimiyar Ingila dai a yanzu ita ce ta 5 a teburin gasar, da tazarar maki 11 tsakaninta da Liɓerpool da ke jagorantar teburin gasar a yanzu.

Guardiola ya ce za su tattauna da shugabannin ƙungiyar idan har akwai yuwuwar cefano ’yan wasa, a kasuwar cinikayyar ’yan wasa da za a buɗe a watan Janairu mai zuwa.

Haka nan ya buƙaci magoya bayan ƙungiyar su marasa musu baya a wasan da za su yi da Forest a gobe, wacce ke biya mata da tazarar maki ɗaya rak a teburin gasar Firimiyar Ingila

By ukarofi