DAGA MUKHTAR YAKUBU
Kamar dai kowacce shekara, a bana ma an yi taron bikin Kalankuwar Afirika mai taken KILAF AWARD 2024 wanda ake gudanarwa a Kano wanda a bana she ni karo na 8 wato ‘Kano Indigenous Languages of Africa film Market & Festiɓal’.
A ranar Litinin 25 ga Nuwamba 2024 aka fara gudanar da bikin inda aka shafe tsawon kwanaki 5 ana yi.
A rana ta farko dai an buɗe taron ne da yin lakcoci a sahin koyar da aikin jarida na Jami’ar Bayero in da manyan masana a kan aikin jarida da kuma harkar fim suka gabatar da jawabai na tsawon wuni guda.
Haka nan a wani bange kuma an buɗe taron hosarwa a kan harkar fim da kasuwancin sa wanda yake shi ɓangare biyu ne, akwai babban aji da kuma ƙaramin aji a sashin koyar da ilimin harkar Kasuwanci na ɗagote duk dai a cikin Jami’ar Bayero.
Da yamma kuma an gudanar da taron liyafar maraba da baƙi a gidan cin abinci na Gusto da ke cikin Unguwar Nassarawa GRA.
A wajen liyafar cin abincin dai shugaban gudanar da taron, Malam Abdulkareem Muhammad ya gabatar da jawabin maraba da baƙi, Inda a cikin jawabin yake cewa,
“Muna godiya ga Allah da ya nuna mana wannan rana da za a fara wannan taro na Kalankuwar Afirika wanda har ma ya zama al’adarmu a duk shekara Allah yana bamu damar gudanar da shi. Kuma abin farin ciki da alfahari baya ga ilimin da ake samu taron ya zama wani dandamali na sada zumunta a tsakanin mu, da kuma ƙulla abota.
A yanzu ga shi mun haɗu a waje guda cikin jin daɗi da farin ciki tare da rungumar juna. Kuma ko ba komai wannan abin alfahari ne a gare mu mu ‘yan Afirika da muke yare da al’adu mabambanta yau ga shi mun haɗu domin musayar ra’ayi da kuma sada zumunta.
Muna yi wa baƙinmu maraba da suka zo daga ƙasashe masu nisa da waɗanda suka zo daga kusa kamar makwaftan mu Nijar da Kwatano. Haka nan muna yin maraba da baƙinmu da suka zo daga jihohi daban-daban har ma waɗanda suke nan garin Kano. Mun gode Allah ya sa a yi taro lafiya a gama lafiya, kuma Allah ya mayar da kowa gidan sa lafiya.”
Taron dai ya samu halartar Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano Baba Halilu Dantiye da Kwamishiyar Ma’aikatar Al’adu da yawon buɗe Ido, Hajiya Ladidi Ibrahim Garko tare da sauran manyan baƙi.
An ci gaba da taron a rana ta biyu wato talata 26 ga Nuwamba 2024 in da a wannan rana taron ya ci gaba a tsangayar koyar da aikin jarida da ke Sabuwar Jama’ar Bayero da ke Kano.
Abubuwan da suka gudana a rana ta biyun sun haɗa da gabatar da jawabai daga masana harkar yaɗa labarai da kuma ilimin harkar fim.
A taron dai an yi musayar ra’ayi da kuma fahimtar da juna ilimi a kan yadda ci gaban harkar fim ya kai a duniya da kuma irin hanyoyin da masu buƙatar cin gajiyar sana’ar fim ya kamata su bi domin cin moriyar ta.
Haka kuma an bayar da dama ga mahalarta taron da su yi tambayoyi a kan duk wani abu da ya shige musu duhu, saboda taron an shirya shi ne domin bayar da ilimi don haka kada kowa ya ɓoye ko ya ji kunyar tambaya a kan duk wani abu da bai fahimta ko ya shige masa duhu.
A ɓangare guda kuma ana ci gaba da taron bita da kuma horaswa a babban aji wato ‘Master Class’ wanda shi ma wani ɓangare ne da aka tsara gudanarwa a cikin jadawalin bikin, wanda shi kuma aka tsara sai mutum ya yi rajista zai samu shiga, saboda ilimin da ake bayarwa na daban ne, sannan idan aka kammala za a bayar da katin shaida da zai nuna ka samu ƙwarewa a fannin ilimin harkar fim.
Bayan kammala jawaban kuma da ƙarfe biyar na yamma aka fara kallon fim ɗin ‘Princess Of Galma’ na kamfanin Jammaje wanda fim ne na sarautar gargajiyar Hausa da ya bada labarin tsarin masarautar ƙasar Hausa da kuma al’adu da zamantakewar al’ummar Hausawa. Amma dai a cikin harshen turanci aka yi fim ɗin. Don haka Bahaushen fim ne da yaren turanci.
An dai shafe tsawon sa’o’i biyu ana kallon fim ɗin, kuma daga baya aka yi tambayoyi ga furodusan fim ɗin Kabiru Musa Jammaje da kuma daraktan fim ɗin Galadima Muhammad. Hakan kuma shi ne ya kawo ƙarshen taron na rana ta biyu da misalin ƙarfe bakwai na dare.
A rana ta uku an ci gaba da gabatar da taron bikin KILAF AWARD, al’amura sun ci gaba da gudana na jadawalin bikin, inda a wannan rana aka yi bita a kan ilimin bayar da umarni a fim da yadda ya kamata mai bayar da umarni ya kasance a tsakanin sa da furodusa, jarumi da kuma sauran masu ruwa da tsaki a cikin fim ɗin da yake bayar da umarni.
Dakta ɓictor Okhai, shi ne ya fara gabatar da ta sa bitar da safe zuwa ƙarfe 2:30 na rana, inda aka rufe da tambayoyi da kuma bada amsa.
Bayan ya kammala ne, sai kuma tawagar mahalarta taron suka halarci gidan Shugaban ƙungiyar Dattawan Arewa reshen Jihar Kano, Dakta Gwani Umar Faruk da ya shirya liyafar cin abinci ta musamman, domin yi wa baƙin da suka halarci taron maraba da nuna farin cikinsa.
A gidan nasa da ke Titin Sokoto a Unguwar Nassarawa G R A a Kano, an ci abinci na gargajiyar Hausa da sauran kayan ƙwalam da makwulashe, inda aka rufe da addu’a da misalin ƙarfe uku na rana.
Bayan an dawo wajen taron da ake gudanar da shi a tsangayar koyar da aikin jarida da ke Sabuwar Jama’ar Bayero. An ci gaba da gabatar da taron karo na biyu.
A ci gaba da gudanar da taron darakta Nasiru B Muhammad, ya jagoranci koyar da yadda za a yi aikin bayar da umarni da kuma ayyukan da suke kan darakta.

Haka nan ya bayar da misalai da dama na yadda ake samun kura-kurai a cikin aikin bayar da umarni a finafinan Hausa, kuma mafi yawan matsalar tana faruwa ne ta yadda shi darakta bai san aikin sa ba. Baya ga haka sai kaga darakta yana aikin amma bai karanta labarin da yake bayar da umarni ba, don haka dole a rinƙa samun matsala. Kuma babbar hanyar da za a magance wannan matsala ta ce, ilimin aikin da sanin abin da ya kamata a yi. An rufe taron da misalin ƙarfe shida na yamma, bayan an kammala bayar da amsoshin mahalarta taron.
An ci gaba da gabatar da jawabai tare da bayar da horo a taron KILAF AWARD 24 a rana ta huɗa ta gudanar da taron wato Alhamis 28 ga Nuwamba 2024 a babban ɗakin taro na Tsangayar koyar da aikin Jarida da ke Sabuwar Jama’ar Bayero, Kano.
Za mu ci gaba a mako mai zuwa da yardar Allah.
