Daga AISHA ASAS
Sau da yawa shahara kan mantar da masu ita cewa, wata rana mabiyan nan nasu da ke ji tamkar su dafa namansu su ba su don kauna, za a waye gari sun manta da su, watakila da suna wannan tunanin, da dayawa sun yi wa irin wannan lokacin tanadi.
Shahararriyar jarumar barkwanci da ta jima tana saka zukatan masu kallonta farinciki na ɗaya daga cikin jaruman da ke da hangen nesa, domin tuni ta san soyayyar mabiya ba dawamamma ba ce, don haka ne ma ta sanar da ‘yarta wannan darasi tun kan ranar ta zo.
Christy Ndubueze, ɗiya a wajen marigayiya Miss Americana, ta bayyana ɗaya daga cikin maganganun hikima da mahaifiyarta ke yi mata, waɗanda a yanzu ne take sanin ma’anarsu.
“Mahaifiyata ta taɓa gaya min, soyayyar mabiya na samuwa ne kawai a lokacin da suke ganinka. Da farko ban fahimci abinda take nufi ba, sai da ta mutu ne na fahimci kalamanta, ganin yadda ‘yan Najeriya suka manta da ita tamkar ba ta taɓa nishaɗantar da su ba,” cewar ‘yar Miss Americana.
Ta ƙara da cewa, “Mahaifiyata mace ce mai matuƙar iya barkwanci, wadda ta yi tashe har take haskawa da manyan jarumai irin su; Mista Ibu, Ukwa, Sam Loco, da kusan dukka manyan jarumai da ake tinƙaho da su yanzu.
Kusan kowa ya san Miss Americana, amma abin mamaki, lokacin da ta mutu, babu ko ɗaya daga cikin abokan sana’arta da ya aika da saƙon ta’aziyya ga iyalanta.
Zan iya tunawa a wani lokaci da duniyar ta yi mana tsanani, ta taɓa sake faɗin cewa, mabiyanka za su yi ta yabonka da nuna maka kauna, amma fa ba daga zuciyarsu take fitowa ba, domin da zaran an daina ganinka a talabijin, to fa za a nemi wannan soyayyar a rasa.
Ban tabbatar da gaskiyar maganar ta ba, sai bayan mutuwar ta, naga zahiri.
Abin takaici ne yadda duniya ta koma duba matsayinka kafin a taimaka maka. Ko hangen amfaninka kafin a kai ma agaji.”
