Ganduje na yunƙurin kama kakakin gwamnan Kano

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Babban Daraktan yaɗa labarai da sadarwa na Gwamna Abba Yusuf, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana yadda ya nemi mafaka a gidan gwamnatin Jihar Kano domin gudun kada jami’an ƴan sanda su kama shi.

Da ya ke magana a ranar Asabar yayin taron ƙungiyar sadarwar matasa ta ‘PR Nigeria’ a Kano, Bature Dawakin Tofa ya yi ikirarin cewa kimanin jami’ai 40 daga tawagar Sufeto Janar na ƴan sanda (IGP) aka tura Kano kwanaki shida da suka gabata da nufin cafke shi.

“Kwanaki biyar da suka gabata, ina gidan gwamnati kuma na kasa fitowa”, inji shi.

Dawakin Tofa ya ƙara da cewa, ya zaɓi gidan gwamnati ne a matsayin wuri da zai iya samun mafaka saboda kariyar da tsarin mulki ya ba ta, wanda ke hana kamawa a harabar gidan ba tare da amincewar gwamna ba.

Ya kuma bayyana cewa ya samu umarnin kotu da ya hana ƴan sanda kama shi.

Jaridar Kano Times ta ruwaito cewa Sunusi Bature ya zargi shugaban Jamiyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje da tura jami’an tsaro 46 ɗauke da makamai domin kama shi.

Dawakin Tofa ya yi zargin cewa Ganduje ya aikata hakan ne daga rahotannin dakatar da shugaban jam’iyyar APC da shugabannin mazaɓunsa suka yi.

Saidai kuma wata babbar kotun Kano ta hana Sufeto Janar na ƴan sanda da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da sauran jami’an tsaro tsare kakakin na Gwamna.

By Babaji