
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Tarayya ta musanta ikirarin da wasu hukumomin ƙasar suka yi na cewa tana da hannu a harin 13 ga watan Disamba da aka kai wa bututun mai na Nijar-Benin dake Gaya, yankin Dosso da Jamhuriyar Nijar.
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje, Kimiebi Ebienfa, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya ce Gwamnatin Nijeriya ta musanta kowane irin alaƙa da ƙungiyar ta’addanci ta Lakurawa ko zargin jami’anta suna da hannu a lamarin.
Ƙasar ta jajenta wa Nijar game da harin tare da jaddada ƙoƙarinta wajen daƙile ta’addanci da ƙaurace wa kusanci da ire-iren waɗannan ƙungiyoyin.
Ministan Harkokin Waje na Nijar ya zargi Nijeriya da zama mafaka kuma wadda za ta taimaka wajen haddasa tashin-tashina a ƙasar, kamar yadda gidan telebijin na ƙasar ya bayyana.
A ƴan kwanakin nan ne Nijeriya ta musanta cewa akwai sansanin sojojin Faransa a arewacinta wanda aka yi zargin cewa an samar da shi ne don haifar da tarzoma a Nijar.
Saidai Nijeriyar ta ƙaryata zarge-zargen tare da yin watsi da su, ta na mai kira ga al’umma da su yi watsi da su.
Sanarwar ta ƙara da cewa akwai alaƙa mai kyau da mutuntawa tsakanin Nijeriya da Faransa, amma ban da shiga harkokin cikin gida.
Kazalika Nijeriya za ta cigaba da kula da zaman lafiyar da ke tsakanin ta da Nijar da kyakkyawar alaƙarsu don amfanin al’ummominsu baki ɗaya.
