Tinubu ya umarci sojoji su kawo ƙarshen ta’addanci a 2025, inji Ministan tsaro

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Shugaba Bola Tinubu ya umurci sojojin Nijeriya da su tabbatar da kawo ƙarshen ayyukan ƴan ta’adda kafin shekarar 2025, kamar yadda ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Mohammed Matawalle, ya bayyana.

Matawalle ya bayyana hakan a ranar Asabar yayin da yake jawabi ga ƴan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a gidansa da ke Gusau, inda ya yi alƙawarin cewa sojoji za su yi duk abin da ya dace don bin umarnin Shugaban Ƙasa.

Tsohon gwamnan Jihar Zamfara ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta kammala shirye-shiryen tura ƙarin sojoji da kayan aikin soji zuwa yankunan da matsalar tsaro ta fi ƙamari a shiyyar Arewa maso Yamma.

“Hankalin Gwamnatin Tarayya da shugabannin sojoji ya tashi sosai kan batun masu ba da bayanai wa ƴan ta’adda.

“Wannan shi ne babban ƙalubalen da ya hana cin nasara kan ƴan ta’adda,” in ji shi.

Matawalle ya bayyana takaicinsa kan yadda wasu daga cikin mazauna al’umma suke zama masu ba da bayanai wa ƴan ta’adda, suna siyar da lamirinsu ga shaiɗan don samun kuɗi.

By ukarofi