Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) sun kama wani ɗan kasuwa, Olisaka Chibuzo Calistus, a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano da ke Jihar Kano.
Ana zargin wanda aka kama, wanda ya ce yana aikin shigo da kaya da fitar da su, da ɗauke da ƙwayoyi 256 na hodar iblis masu nauyin kilogiram shida a ranar Lahadi, 15 ga Disamba.
Kakakin NDLEA, Femi Babafemi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi.
“Wannan kamen, wanda shi ne mafi girma tun da aka kafa ofishin hukumar NDLEA a filin jirgin sama na Kano a 2006, an yi shi ne a ranar Lahadi 15 ga Disamba 2024 yayin binciken fasinjoji da suka iso da jirgin Ethiopian Airlines ET 941 daga Abidjan, Côte d’Ivoire daga Addis Ababa, Ethiopia,” in ji sanarwar.
“Olisaka wanda ya ce shi ɗan kasuwa ne mai shigo da kaya da fitar da su, an yi masa binciken jiki inda aka gano ɗaruruwan ƙwayoyi a jikinsa.”
Haka kuma, Babafemi ya bayyana cewa hukumar ta daƙile wani yunƙuri makamancin wannan da wani mai suna Olanrewaju Bada Akorede, ya yi na fitar da ƙwayar Rohypnol zuwa Afirka ta Kudu ta sashin kaya na filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas.
An ce an ɓoye ƙwayoyin ne a cikin kaya da suka haɗa da gari, takalma, rigunan maza da sauran abubuwa.
A cewar sanarwar, Olanrewaju ya taɓa yin irin wannan laifin a bara inda aka kama shi a ranar 12 ga Disamba 2023 lokacin da yake ƙoƙarin fitar da tramadol mai nauyin kilogiram 4.90 da Rohypnol mai nauyin kilogiram 2.10 zuwa Afirka ta Kudu ta sashin kaya na filin jirgin sama na Lagos.
“An yanke masa hukuncin zama gidan yari na tsawon shekara biyu a Babbar Kotun Tarayya da ke Lagos tare da zaɓi na biyan tarar Naira 900,000, wanda ya biya, aka sake shi kafin ya koma yin irin wannan laifi.”
Haka zalika, wata ‘yar kasuwa da ke zaune a Italiya, Cynthia Akaeen, an kama ta a ranar Laraba 18 ga Disamba, lokacin da take ƙoƙarin shiga jirgin Royal Air Maroc zuwa Italiya ta Addis Ababa.
Jami’an NDLEA sun cafke ta ne a wurin fasinjoji masu fita a Terminal 2 na filin jirgin sama na Legas yayin da suke binciken fasinjoji da za su tafi Italiya.
“An gano ƙwayoyi 9,190 na tramadol daban-daban masu nauyin kilogiram 6.00 tare da ita. A cewarta, an yi mata alƙawarin samun Yuro 1,000 idan ta yi nasarar isar da kayan a Italiya,” in ji Babafemi.
