Tare da MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI
Illar istimnati ga ƙwaƙwalwa:
ƙwaƙwalwar mutum ita ce cibiyar gudanar da dukkan ayyukan jikinsa ko jikinta. Yawan aikata wannan aiki ya na jawo matsaloli ga ƙwaƙwalwa. Yana da illoli da yawa, amma na tsamo manya guda hudu, su ne:
1. Jaraba
2. Mantuwa
3. Rashin mayar da hankali
4. Damuwa
Zan yi bayanin kowanne a taƙaice.
1. Jaraba
Jaraba ko kuma addiction a turance shi ne tsananin shaƙuwa da wani abu, ko wata halayya, ko wata ɗabi’a. Idan mutum ya na istimna’i, babu wahala jarabar aikata wannan ɗabi’a ta kama shi. Mutum ba zai taɓa jin daɗi ba har sai ta aikata ko ya aikata. A can cikin zuciyarsa/ta kuwa, su na so su daina amma sun kasa. Wannan shi ne jaraba.
Bincike ya nuna abinda ke jawo hakan shi ne duk lokacin da mutum ya yi wani abu wanda jikinsa ya ji daɗinsa, to ana tsarto da wani sinadari daga ƙwaƙwalwa wanda ake kira dopamine. Shi ne ke da alhakin gamsuwa da jin dadi da mutum yake ji idan ya yi jima’i, ko ya cimma wani abu da yake so. Ita kuwa ƙwaƙwalwa ta na adana duk wani abu da ya sami ɗan adam imma na jin daɗi ko akasinsa. Idan na jin daɗi ne, to za ta sanya ki/ka bin duk wata hanya da za ta kaiku aikata wannan abu ko da kuwa ya na illa, inda a ƙarshe za a ji daɗin a rai da jiki, to magana ta ƙare.
Shi yasa yaƙi da abinda ya ke ba wa ƙwaƙwalwa jin daɗi ya ke da wahala. Daina shan taba da wahala, daina bin mata da wahala, daina shan giya da wahala, haka ma daina yin istimna’i da wahala amma kuma a na iya daianwa.
A cikin nazari na, akwai labarin da naci karo da shi cewa wasu ƙalilan daga mashaya giya sukan mace har lahira a sakamakon wasu wahalhalu ko tsabar jaraba da sukan fuskanta saboda sun dena sha, amma hakan ba ya nuna cewa mutum ba zai iya dainawa ba, matuƙar an bi matakan dainawa waɗanda zan kawo nan gaba kaɗan in sha Allah. Ku biyo ni.
Naku, Mustapha Ibrahim Abdullahi
©MIAbdullahi 2024
