Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Jihar Legas ta rufe wasu cibiyoyi da suka haɗa da coci-coci, otel-otel, da wuraren shaƙatawa, saboda karya wasu ƙa’idoji da hayaniya da sauran abubuwan da suka shafi muhalli.
Hukumar Kare Muhalli ta Jihar Legas (LASEPA), ce ta ɗauki matakin aiwatar da aikin, kamar yadda aka bayyana a shafin hukumar na Tuwita a ranar Litinin.
A cewar hukumar, laifuffukan cibiyoyin na haifar da babbar illa ga lafiyar jama’a da tsaro.
Wuraren da abin ya shafa sun haɗa da Shomolu, Oniru ɓictoria Island, Jakande-Lekki, Badore Ajah, Lekki-Epe Eɗpressway, Sangotedo, Lekki II, Ogombo, da Lekki Phase 1, da dai sauransu.
Wadɗannan sana’o’in da suka haca da coci-coci, otel-otel, wuraren kwana, da gidajen cin abinci, an gano cewa suna bayar da gudunmawa wajen yawan hayaniya da kuma yin wasu ayyuka masu illa ga muhalli, wanda hakan ya sa hukumar ta LASEPA ta yi gaggawar shiga tsakani.
“Hukumar Kare Muhalli ta Jihar Legas (LASEPA) ta ƙara ƙaimi wajen aiwatar da ayyukanta ta hanyar rufe wasu cibiyoyi a wurare daban-daban a jihar.
“An ɗauki matakin ne domin mayar da martani ga dakatar da hayaniya da sauran munanan abubuwan da ke haifar da haɗari ga lafiyar jama’a da tsaro.
“Yankunan da abin ya shafa sun haɗa da; Shomolu, Oniru ɓictoria Island, Jakande-Lekki, Badore Ajah, Lekki-Epe Eɗpressway, Sangotedo, da Lekki II, Ogombo, Lekki Phase 1 da dai sauransu,” sanarwar ta kara da cewa.
Sanarwar ta jadadda cewa waɗannan ayyukan tilastawa sun yi nuni da ƙudirin hukumar na kiyaye muhalli mai kyau, tare da lura da cewa hayaniya da sauran abubuwan da suka saɓa wa muhalli suna kawo cikas ga zaman lafiya da lafiyar al’umma.
