Turmutsutsun Ibadan: Peter Obi ya nemi a sako tsohuwar matar Ooni na Masarautar Ife

Spread the love

Daga BELLO A BABAJI

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jami’yyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi ya yi kira ga gwamnati da ta sako Misis Olori Naomi Silekunola, wadda tsohuwar matar Ooni ce na Masarautar Ife da wasu mutane bakwai da aka kama da hannu a turmutsutsun Ibadan.

Iftila’in ya auku ne a ranar 18 ga watan Disamba inda aka rasa rayukan yara 35 da wasu shida da suka samu raunuka a makarantar Islamic High School dake Bashorun ta babbar birnin jihar Oyo.

Gidauniyar ‘Wings’, wadda take taimaka wa matan aure da mata ta ɗauki nauyin taron ne da nufin samun halartar aƙalla mutane 5,000.

A ranar 19 ga wata Disamba ne rundunar ƴan sandan jihar ta fitar da sanarwar cewa ta kama Misis Silekunola wadda ita ce ta ɗauki nauyin shirin da shugaban makarantar da wasu mutane shida.

A cikin wani saƙon da aka wallafa ta kafar X a ranar Lahadi, Obi ya miƙa gaisuwar ta’aziyyarsa ga iyalai, garuruwa da ma jihar game da waɗanda suka rasa rayukansu yayin rabon kayayyakin tallafi.

Ya koka kan yadda mutane suke rububin zuwa karɓar kayan tallafi ganin yadda yunwa da talauci ke cigaba da addabar su a ƙasar.

Game da kama tsohuwar matar Oonin, Obi ya yi kira ga gwamnati da ta sake nazari, ya na mai cewa kada a mayar aikin alheri wanda an samar da shi don rage raɗaɗin halin matsi da ake ciki, ya zama babban laifi.

Ya kuma yi kira ga jagorancin al’umma da su yi duba game da asalin dalilan da suka haddasa yunwa da talauci a Nijeriya tare da ɗaukar matakan magance su.

By Babaji