
Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma ƙaramin ministan Tsaro, Hon. Bello Mohammed Matawalle ya musanta rahotannin da ke cewa ƴan bindigar Lakurawa na cikin jihar Zamfara.
Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidansa dake Gusau, babban birnin jihar jiya lahadi.
A cewarsa, sojoji sun fatattaki ‘yan bindigar Lakurawa kafin su samu shiga kowacce jiha a yankin Arewa maso Yamma.
“Tun bayan bullar ‘yan bindigar Lakurawa, ba su da wani sansani kuma suna tafiya da dukkan kayansu ne a lokaci guda, kuma cikin ikon Allah maɗaukakin Sarki, sojojin Najeriya sun samu gagarumar galaba a kansu.”
Ministan ya kuma ce, gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu tana aiki ba dare ba rana domin ganin an samu zaman lafiya a yankin Arewa maso Yamma.
Ya yi kira ga al’ummar jihar Zamfara da ɗaukacin yankin Arewa maso Yamma da su ba gwamnatin tarayya haɗin kai don samun sukunin aiwatar da tsare-tsare na ci-gaban jihar da kuma yankin baki daya.
Ya yabawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa bada kwangilar gina tagwayen titin daga Zaria-Funtua-Gusau zuwa Sokoto, inda ya ce idan aka kammala aikin, jihohin Kaduna, Katsina da Sokoto za su bunƙasa ta fuskar zamantakewa da tattalin arziƙi.
