‘Yan sandan Kano sun gargaɗi masu tare hanya don ɗa ukar bidiyon barkwancin yanar gizo

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Rundunar ƴan sandan jihar Kano sun gargaɗi ƴan wasan barƙwanci game da ɗaukar bidiyo akan titina wanda hakan ke haifar da cinkoson ababen hawa.

Rundunar ta lura cewa cinkoson ababen hawa a musamman manyan titina saboda ire-iren ayyukan wanɗanda saɓa wa dokar ƙasa ne ka iya haifar da hatsari.

Don haka ne take gargaɗin al’umma da su ƙaurace wa aikata hakan, ta na mai kira ga iyaye da su ja wa ƴaƴansu kunnuwa kan shiga irin ayyukan.

Ta kuma ce tana cigaba da tabbatar da zaman lafiya acikin al’umma ta hanyar ɗaukar matakan da suka dace wanda acikin hakan akwai kama waɗanda suka aikata laifuka.

Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Salman Dogo Garba ya yi kira ga al’umma da su riƙa ruwaito wa hukumar duk wani abu da zai haifar da tsaiko ga zaman lafiyarsu.

By Babaji