Super Eagles za ta samu nasarara zuwa gasar kofin duniya na 2026 – Shugaban NFF

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaban Hukumar Ƙwallon ƙafa ta Ƙasa (NFF), Alhaji Ibrahim Musa Gusau ya bai wa ƴan Nijeriya tabbaacin cewa Super Eagles za ta yi nasarar shiga gasar kofin duniya na 2026 da za a yi a ƙasashen ‘Mexico’ da Amurka da kuma ‘Canada’.

Ya kuma tabbatar da cewa su na ƙoƙarin samar da ci-gaba daga tushe a harkar ƙwallon ƙafar Nijeriya.

A lokacin da ya ke jawabi yayin wasan ƙarshe na kofin ciyaman da Hukumar Ƙwallon ƙafa ta Sakkwato ta shirya, Alhaji Gusau ya yaba mata bisa nasarar shirya gasar.

A wasan ƙarshe, ƙungiyar Lokoja FC ta doke AA Star be a bugun fenareti bayan tashi wasa 2 da 2.

Shugaban na NFF ya ce akwai takaici ace Nijeriya ta rasa damar shiga gasar har sau biyu a jere, ya na mai cewa akwai buƙatar yin aiki kafaɗa-da-kafaɗa tsakanin masu-ruwa-da-tsaki domin kai ta ga nasara.

By Babaji