DMCSA za ta haɗa hannu da NDLEA don yaƙi da miyagun ƙwayoyi

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Hukumar Samar da Magunguna da Kayan Aikin Asibiti ta Jihar Kano, DMCSA ta nemi haɗin kan Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta ƙasa, NDLEA reshen Kano don yaƙar mummunar ta’adar nan ta ta’ammali da miyagun ƙwayoyi musamman a tsakanin ma’aikatan gwamnati.

Shugaban DMCSA, Famasist Gali Sule ne ya bayyana haka yayin da ya kai ziyarar aiki zuwa ofishin NDLEA dake nan Kano a safiyar ranar Litinin.

Ya nuna damuwarsa sakamakon yadda shan miyagun kwayoyi ya zama ruwan-dare musamman a tsakanin matasa, a faɗin jihar.

Shugaban ya ce za su yi wa dukkanin ma’aikatan hukumar, ciki har da shugannin ma’aikatar, gwajin shan miyagun ƙwayoyi domin tabbatar da ɗa’a.

”Hukumarmu za ta shirya taron wayar da kai a kan illar shan miyagun ƙwayoyi, inji shi.”

Da yake jawabi, Kwamandan NDLEA a Kano, Abubakar Idris Ahmad, wanda ya sami wakilcin muƙaddashinsa, Yaya Muhammad Aminu, ya ce ma’aikatarsa a shirye take domin haɗa kai da DMCSA domin yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.

Ya kuma yaba wa Famasist Gali Sule bisa hagen nesansa da zai kai su ga nasara a yayin ayyukansu.

By ukarofi