Hukumar NCAA ta sanya takunkumi kan Ethiopian Airways, Arik da Air Peace

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Nijeriya (NCAA) ta fara ɗaukar matakin ladabtarwa kan kamfanonin jiragen sama guda biyar (Na ƙasashen waje guda biyu da na cikin gida uku) bisa saɓa wa sashe na 19 na dokokin NCAA.

Laifukan sun haɗa da rashin biyan kuɗi cikin lokacin da aka ƙayyade, rashin bin umarnin hukumar ta NCAA, da ɓacewar jakunkuna kwastomomi, da jinkiri da soke tafiyar jirgi da dai sauransu.

Kakakin hukumar ta NCAA, Michael Achimugu ne ya bayyana hakan ga manema labarai a hedikwatar hukumar da ke Abuja ranar Talata.

Yayin da Achimugu bai bayyana kamfanonin jiragen da ya sanya wa takunkumi ba, majiyoyin da ke kusa da Hukumar sun shaida wa manema labarai cewa kamfanonin jiragen da aka sanya wa takunkumin sun haɗa da; Ethiopian Airways, Royal Maroc Airways, Arik Air, Aero Contractors, da Air Peace.

Ya ce, duk da cewa kamfanonin jiragen sama ba koyaushe ne ke da alhakin kawo cikas ba, amma dokokin hukumar ta NCAA sun tanadi matakan da ya kamata kamfanonin jiragen su yi a lokacin da ake samun matsala. Rashin yin biyayya yana jawo matakai daban-daban na takunkumi.

By ukarofi