Sufeto Janar ya musanta umartar ’yan Nijeriya su doki jami’ansa bisa binciken wayoyi

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta ce babban sufeton ’yan sandan ƙasar, Kayode Egbetokun, bai umurci ‘yan Nijeriya da su riƙa kai wa jami’an hari ba a lokacin da suke gudanar da bincike.

A cikin wata sanarwa a ranar Litinin, kakakin rundunar, Muyiwa Adejobi, ya ce Egbetokun bai taɓa ƙarfafa cin zarafin jami’an tsaro ba.

Sanarwar ta ce “Rundunar ‘yan sandan Nijeriya na son yin magana kan wani labari na ƙarya da ya ɓullo, yana mai cewa sufeto-Janar na ‘yan sanda, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, ya umurci ‘yan ƙasar da su riƙa cin zarafi da jifa duwatsu ga jami’an ‘yan sanda da suka nemi su bincika wayoyinsu.

“Wannan ikirari gabaɗaya ƙarya ce kuma ba ta da tushe a zahiri.

“IGP ɗin bai bayar da irin wannan umarnin da ke ƙarfafa cin zarafin jami’an tsaro ba.

“Maimakon haka, ya yi kira ga ‘yan ƙasa da su kai rahoton rashin ɗa’ar ‘yan sanda ta hanyoyin da suka dace.

“Wannan hanya tana nuna muhimmancin bin diddigi da kuma kiyaye doka da oda, maimakon aiwatar da ayyukan tashin hankali.

“An shawarci jama’a da su yi taka tsantsan game da bayanan da ba su dace ba kuma su tabbatar da bayanai ta hanyar sahihan bayanai.”

NPF ta ce, ta ci gaba da jajircewa wajen samar da haɗin kai da aminci tsakanin ‘yan sanda da al’ummomin da suke yi wa hidima.

By ukarofi