Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
An shiga zaman ɗar-ɗar a ƙaramar hukumar Kaugama da ke jihar Jigawa bayan da makiyayan suka yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da kwace musu gonakin da wani kamfanin noman shinkafa ya yi.
Wani faifan bidiyo na wasu makiyayan ya bayyana a yanar gizo inda ya nuna wani mummunan artabu tsakanin makiyayan da jami’an da ke aiki a dajin Marke.
Rahotanni sun ce gwamnatin jihar ta ware dajin ne ga wani kamfani na noman shinkafa amma makiyayan sun ce sun gaji wannan fili kuma sun yi amfani da shi tsawon shekaru aru-aru. Don haka, ba za a iya soke mallakarsu dare ɗaya ba.
“Ta yaya za ku zo dare ɗaya ku ce mu bar gidajenmu? Ba za mu yarda da hakan ba,” inji ɗaya daga cikin masu zanga-zangar a cikin bidiyon.
Wata mata mai zanga-zangar ta ce kakanninsu haifaffun yankin ne amma an ce musu su tattara kayansu su fice.
Da take mayar da martani kan faifan bidiyon, ƙungiyar al’adun Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore ta buƙaci gwamnati ta magance koke-koken makiyayan.
Shugaban ƙungiyar a jihar, Umar Kabiru ya ce ungiyar ta samu labarin cewa gwamnati ta bayar da filin ne ga wani kamfanin shinkafa.
“A matsayina na shugaban Fulani a jihar, wannan lamari ne mai tayar da hankali a gare ni, domin irin wannan lamari yakan haifar da rikici a cikin al’umma. Muna fatan za a magance lamarin kafin ya koma wani abu na daban.
“Muna sane da ƙudirin gwamnatin nan na magance rikicin manoma da makiyaya. Manufar gwamna na gaggawar mayar da martani ga irin wazannan rikice-rikice yana da muhimmanci. Mun kai rahoto ga gwamnati kuma muna sa ran za a mayar da martani mai kyau,” inji shi.
Babban Sakataren Hukumar Manoma da Makiyaya ta Jihar Jigawa, Salisu Abdullahi, ya ce gwamnatin jihar ta bayar da umarnin dakatar da aiki kan filin da ake taƙaddama a kai tare da bayar da umarnin gudanar da bincike.
