Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban Jam’iyyar APC mai mulki, Dokta Abdullahi Ganduje, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya su ci gaba da haƙuri da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, yana mai tabbatar musu cewa tattalin arzikin ƙasar zai daidaita nan da Kirsimeti mai zuwa.
A cikin saƙon Kirsimeti da aka fitar a ranar Laraba ta hannun Mai Magana da Yawunsa, Edwin Olofu, Ganduje ya nuna ƙwarin guiwa game da farfaɗowar tattalin arzikin ƙasa. Ya amince da wahalhalun da ake fuskanta sakamakon sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnati ta aiwatar, amma ya tabbatar wa ‘yan ƙasa cewa alamun nasara sun fara bayyana.
“Ina kira ga ‘yan Nijeriya su ƙara haƙuri da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu yayin da take gudanar da waɗannan manyan sauye-sauyen. Ko da yake hanyoyin sun kasance masu wahala, amma muna fara ganin sakamako masu kyau,” inji Ganduje.
“Nan da Kirsimeti na baɗi, ina tabbatar muku, tattalin arzikin zai daidaita kuma zai kasance a matsayi mafi kyau.”
Ganduje ya kuma jaddada ci gaban da gwamnatin ta samu wajen inganta harkar tsaro, inda ya bayyana raguwar yawan satar mutane da hare-haren ‘yan fashi a sassan ƙasar.
