Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), reshen jihar Kano, ta kama mutane 34 da aka samu da nau’ikan miyagun ƙwayoyi daban-daban a jihar.
Kakakin hukumar, ASN Sadiƙ Muhammad-Maigatari, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Laraba a Kano.
Muhammad-Maigatari ya nakalto Kwamandan hukumar a jihar, Malam Abubakar Idris-Ahmad, yana cewa an yi kamen ne yayin wani samame da aka kai, a matsayin ɗaya daga cikin matakan kariya don tabbatar da tsaro da kawar da miyagun ƙwayoyi a Kano yayin bikin Kirsimeti da Sabuwar Shekara.
“A ranar 24 ga Disamba, hukumar ta kore mutane a wasu wuraren da aka daɗe ana safarar miyagun ƙwayoyi a faɗin jihar. Waɗannan wurare sun haɗa da unguwar Fagge, Filin Wasa na Sani Abacha, ɗanagundi, da kuma tsohon sanannen sansanin miyagun ƙwayoyi na Filin Idi.”
Ya ce hukumar ta samu nasarar ƙwato adadi mai yawa na miyagun ƙwayoyi, kamar su tabar wiwi, suck and die, da Eɗol-5, da sauransu.
A cewarsa, wasu kayan da aka ƙwato sun haɗa da makamai masu haɗari da masu safarar miyagun ƙwayoyi ke amfani da su don kawo hari ga jami’an tsaro.
