
Daga BELLO A. BABAJI
A shekarar 1996, wani kamfanin magunguna mai suna Pfizer ya fitar wani magani na yara da ake kira da ‘Trovan’ wanda ya yi sanadiyyar mutuwar yara da dama da kuma nakasa wasu.
Bayan shekaru 28, waɗanda suka tsira daga annobar da maganin ya haifar sun koka da mummunan halin da suka tsinci kawunansu.
A shekarar ne al’ummar Nijeriya musamman ta Arewa, suka fuskantaci tsananin cutar sanyi da ake kira da ‘meningitis’.
News Point Nigeria ta ruwaito cewa, wani rahoto da Hukumar Lafiya ta Duniya WTO ta fitar a watan Maris na 1996 ya ce an samu waɗanda suka kamu da cutar guda 8,423 da kuma waɗanda suka rasa rayukansu guda 1,181 a jihohin Adamawa, Bauchi, Kano, Kaduna, Katsina, Kebbi, Kwara, Neja, Sakkwato da kuma Taraba.
Hakan ya sa gwamnati ta amince wa buƙatar Kamfanin Pfizer ta shigowa Nijeriya domin bai wa waɗanda suka kamu da cutar magani da kuma riga-kafi.
A lokacin da kamfanin ya ƙaddamar da maganin trovafloxacin (Trovan), bai samu tantancewa daga hukumar kula da abinci da magunguna ta Amurka ba wanda a sakamakon haka ne ya yi sanadiyyar mutuwar yara 11 da kuma nakasa wasu da dama.
Kasancewar al’umma sun yi tunanin samun waraka daga cutar, amma sai akasin haka ne ya faru wanda har ya kai ga shari’a tsakanin iyalan waɗanda abin ya shafa da gwamnatin jihar Kano da kuma Pfizer.
Yanzu shekaru 28 kenan, amma waɗanda aka yi wa riga-kafin suna ɗauke da nakasa a tattare da su.
Wata mai suna Ruƙayya Salisu ta koka kan yadda rayuwarta ta zama abin tausayi saboda tasirin riga-kafin a tsawon shekarun da aka ɗauka da ƙaddamar da shi sakamakon nakasa a halittarta da maganin ya sabbaba.
Haka ma iyayen wata mai suna Bilkisu Abbas sun ce an yi wa ƴarsu allurar ne a lokacin da take ƴar shekara uku inda tun daga nan, ba ta iya tafiya da ƙafafunta.
Sannan, wani mai suna Mamman Abdullahi ya ce ƴan uwansa suna zuwa makaranta, amma shi bai iya zuwa saboda nakasar da yake da ita a sakamakon rigakafin.
