NNPP na ƙoƙarin sauke nauyin da al’ummar Kano suka ɗora mata – ’Yankaba

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An bayyana ɗaukar nauyin duba masu larurar idanu kyauta da ba su magani da shugaban ƙaramar hukumar Nasarawa ya yi da aka gudanar a Asibitin Gwagwarwa da cewa koyi ne da yake da Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf na baza ayyuka a ko’ina.

Alhaji Yahuza Adamu ‘Yankaba shugaban jam’iyyar NNPP na ƙaramar hukumar Nasarawa ne ya bayyana hakan.

Ya ƙara da cewa shi kuma shugaban ƙaramar hukumar Nasarawa Ogan ɓoye ya yi amfani da wannan dama ya na ɗaukar marasa  lafiya da basu tallafi kamar yanzu yadda ya ɗauki masu larurar ciwon ido dan ƙoƙarin warware musu matsalolinsu suna fatan Allah ya saka masa da alkhari.

Ya ce ya yi farin ciki da murna da yadda ya ga ɗimbin jama’a sun taru daga sassa daban-daban na ƙaramar hukumar Nasarawa har ma da maƙota maza da mata ana duba larurar idanun su ana yi musu abinda ya kamata don samun waraka.

Shugaban jam’iyyar na NNPP na ƙaramar hukumar Nasarawa Alhaji Yahuza Adamu ‘Yankaba ya ce kwalliya na biyan kuɗin sabulu a zaɓen da al’umma suka yi wa NNPP tun daga matakin jiha har ƙananan hukumomi domin a ƙaramar hukumar Nasarawa ƙarƙashin Hon. Yusuf Imam Ogan ɓoye da zaɓaɓɓun kansiloli da sauran muƙarrabai ana ayyuka na kyautata jin daɗin al’umma.

By ukarofi