Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Ƙungiyar tsoffin ɗalibai na makarantar firamare na masallaci (MOPA) ’yan aji na 88 sun gudanar da taro a karo na farko tun bayan gama makarantar.
Taron da aka gudanar a harabar makarantar ranar Talata ya samu halartar ɗinbin tsoffin ɗaliban maza da mata da suka zo daga sassa daban-daban a ciki da wajen Jihar Kano da wasu daga cikin malamai da suka koyar da su.
Tsoffin ɗaliban yan aji na 88 a taron sun tuna baya da irin rayuwa da sukayi suna ƙananan yara ɗalibai da yanda malaman su suka tafiyar da su da kuma tarbiyantar da su da har mafi yawansu da suke a raye suka kai matsayin da suka kai
Suma wasu daga malaman nasu da suka saura da sun sami halartar taron sun nuna jin daɗinsu da alfahari da ɗaliban nasu.
Malama Fatima Fagge ɗaya daga malamai da suka koyar da ɗaliban ta bayyana cewa a lokacinda suke koyar dasu sun ɗauke su ne a matsayin ’ya’yansu da ƙanne da suke ba su ilimi da tarbiyya domin su zama nagari masu amfani a cikin al’umma sannan ta ja hankalinsu akan su waiwayo su kula da tsofaffin malaman nasu da yawanci sun manyanta sosai kuma suna da buƙatar a riƙa tallafawa rayuwarsu.
ƙungiyar tsarffin ɗaliban na makarantar fiuamare na Masallaci yan aji na 88 a taron sun tallafawa malaman su da buhunan shinkafa da kuɗin cefane.
Tun da farko shugaban riƙo .na ƙungiyar ” MOPA” Alhaji Abba Kurawa a jawabinsa na maraba yace taron shine na farko tun bayan kammala makarantar shekaru 36 da suka gabata.
Ya bayyana cewa ƙungiyar ta soma ne da sunan “MOPA gatan zumunci” sakamakon wasu daga tsoffin ɗaliban da suka haɗa da Umma Madaki da A’isha Wada da Mustapha Musa Soron ɗinki suka yi ƙoƙari suka yi gida a kafar sadarwa wacce ita ta haifar da kafuwar wungiyar har Allah ya basu dama suka shirya wannan taro da gudunmuwar daga yan aji na 88.
Alhaji Abubakar Abba Kurawa ya bayyana cewa manufar ƙungiyar ta MOPA shi ne ƙarfafa zumunci da taimakawa juna da makarantar da malamansu suna rokon Allah ya basu kwarin gwiwa na tabbatar hakan.
Da yake ƙarin haske ga ’yan jarida shugaban riko na MOPA.Alhaji Abubakar Abba Kurawa yace bayan wasu ɗalibai sun fitar da mahaɗa a manhajar WhatsApp sai aka yi shugabanci da zai shirya taro da zumunci da taimakon juna da taimakawa malamai duk da sun nemi taimako a ƙurraren lokaci na haɗa taron amma ɗalibai sun yi ƙoƙari sosai na tabbatar da taron.
Ya ce, an gudanar da taron cikin nasara an haɗu anga fuskokin juna da aka daɗe ba’a gani ba wasu ma sun rasu daga cikin su, sun yi musu addu’a an kuma tallafawa tsofaffin malamansu guda 10 da buhunan shinkafa da kuɗin cefane su kuma tsofaffin ɗaliban yan uwansu a wannan haduwa da suka yi ne za su gane masu buƙata da zasu taimaka musu nan gaba da kuma buƙatar da makarantar ke da su.
Shugaban riƙon ƙungiyar na MOPA.Alhaji Abubakar Ahmad Kurawa ya ce ya gamsu da yanda aka sami yawan tsofaffin ɗaliban da suka halarta duk da cewa a ranar aiki ne kuma kusan karshen watan na ƙarshen shekara dama sun roki Allah kada yasa su ji kunyar kuma gashi anyi taro cikin nasara.
