Yadda shugaban ma’aikatan gwamnan Kwara ya gudanar da lokutan ƙarshe na rayuwar shi

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Rahotanni sun bayyana cewa Marigayi Mahe, yarima kuma ɗan Marigayi Sarkin Ilorin na 10, Mallam Aliyu AbdulKadir, ya rasu yana da shekara 73.

Da yake zantawa da wakilinmu a gidan iyalin mamacin, wani makusanci kuma aminin iyali ya ce,“Alhaji Mahe yana cikin ƙoshin lafiya. A ranar Juma’a, 27 ga Disamba, 2024, mun halarci taron bikin aure a gidan babban limamin Ilorin da kuma a gidan iyalan Belgore.

“Bayan haka, mun halarci sallar Juma’a a masallacin Ansarud-Deen dake kan titin Taiwo, Ilorin. Daga nan kuma muka je hedkwatar shige da fice don ɗaukar hoto domin sabunta fasfonsa da ya ɓace. Yana shirin tafiya umara a Saudiyya idan an gama sabunta fasfon.”

“Daga nan muka wuce gidan iyalinsa inda ya halarci wasu tarurrukan iyali sannan ya tafi wajen misalin ƙarfe 7 na yamma. Ya ci gaba zuwa unguwar Agaka domin ziyartar abokinsa, Alhaji Lawal Baba Ariyibi, sannan ya koma gidansa dake Moro Close, Adewole Estate, Ilorin.”

Da yake magana kan yadda abin ya faru, ya ce, “A ranar Asabar, 28 ga Disamba, 2024, wajen ƙarfe 8 na safe, Alhaji Mahe ya zo gidana dake kan titin New Yidi a cikin mota ya kira ni ta waya daga waje. Da na gan shi, na lura yana da rauni a cikin mota. Na tambaye shi ko akwai wata matsala, sai ya ce: ‘Ba komai, kawai na ji rauni ne a jiki yanzu.’”

“Na ce masa: ‘Don me ba ka kira ni ba don in zo in ɗauke ka daga gida?’ Mun kira wani likita don a tafi asibitin koyarwa na jami’ar Ilorin (UITH), amma Allah ya karɓi ransa kafin mu isa asibitin.”

Marigayi Mahe ya sami jana’iza a gidansa wanda babban limamin Ilorin, Alhaji Muhammad Bashir Imam-Soliu OON, ya jagoranta.

Manyan baƙin da suka halarci jana’izar sun haɗa da Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq, Gwamnan Jihar Kogi, Gwamna Usman Ododo, Mutawallen Ilorin, Dr. Alimi Abdulrazaq, Dr. Ghali Alaaya, Hon. Yinka Aluko, Hon. Ishola Balogun-Fulani, Magajin Muse na Ilorin, Injiniya Abubakar Aduragba, Ɗanmasanin Ilorin, Injiniya Sulyman Alapansapa, Tafidan Ilorin, Alhaji Kawu Baraje, da Ɗanmadamin Ilorin, Alhaji Shehu Gafar, tare da wasu da dama.

By ukarofi