Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Kungiyar ‘yan jarida ta Nijeriya reshen jihar Zamfara masu aikawa da labarai ta taya Hon. Abdulmalik Zubairu mamba mai wakiltar mazaɓar Bungudu da Maru a majalisar tarayya akan naɗin sa a matsayin Mayegun na masarautar Ikare-Okoko a jihar Ondo.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar ta Chapel, Ishaƙ Zaki Tambuwal ya raba wa manema labarai jiya Alhamis a Gusau.
Tambuwal ya bayyana Zannan Bungudu a matsayin ginshiƙin siyasa, mai taimakon jama’a kuma jajirtaccen shugaba mai amfani da dukkan ƙarfinsa wajen yi wa bil’adama hidima.
“A madadin ɗaukacin ‘ya’yan ƙungiyar ‘yan jarida ta NUJ ta Zamfara masu aikawa da labarai, muna taya ka murnar samun sabuwar sarauta a matsayin Mayegun na masarautar Ikare-Akoko” wanda mai martaba Oba Akadri Saliu Momoh Olukare na Ikare-Akoko ya ba ka.
“Muna yi maka fatan alheri, shiriyar Allah da kariyarsa,” inji Tambuwal a cikin sanarwar.
