Abin da ya bambanta Gasar Marubuta ta Gusau Institute da sauran

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

Gasar Tsangayar Gusau ce gasar dogon labari kaɗai da ake yi – Jibrin Adamu Jibrin Rano

Gasar Tsangayar Gusau ta fi ta BBC Hausa – Hassana Suleiman

Idan ka ɗauke Gasar Hikayata ta BBC Hausa wanda ake shirya wa marubuta mata, babu wata gasa da marubutan adabin Hausa ke marmarin ganin zuwan ta kamar Gasar Gusau Institute, wacce Babban Malamin Hausa, Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau ya yi wa laƙabi da Gasar Tsangayar Gusau. Saboda yadda ta sha bamban da sauran gasanni da ake shiryawa duk shekara, don bunƙasa harshen Hausa. 

Da farko dai, Gasar Tsangayar Gusau ba kowanne marubuci ne yake garajen shigarta ba, saboda tsaurinta. Ita ba gasar rubutun Gajeren Labari ba ce, mai ýan kalmomi dubu da ɗari biyar, ko kusa da haka ba. Littafi sukutum ake rubutawa, wanda ba a taɓa rubuta shi ko ɗora shi a wata kafa ba. Sannan somin taɓin farko na labarin da ake buƙatar masu son shiga gasar su fara turawa, shi ma jan aiki ne. Domin kuwa sai marubuci ya yi nazari sosai ta yadda zai iya yin rubutun da zai ja hankali, kuma ya gamsar da alƙalan gasar, har su nemi ya tura da sauran ƙarashen labarin. Waɗanda su kuma suke tsayawa su ƙalailaice jigon labarin da salonsa. Don haka duk wanda aka ce maka gashi ya tsallake dukka matakan alƙalancin gasar har ya kai ga matakin ƙarshe to, dole a jinjina masa, kuma a kalle shi a sake kallon sa.

A tsawon shekaru bakwai da fara wannan gasa, za ka tarar marubutan da suka samu nasara, dukkansu babu kanwar lasa! Gasa ce da ta ƙunshi maza da mata, ba tare da ƙayyade shekaru ba. Ashe kuwa kun san gwagwarmayar ba ƙarama ba ce! 

Kamar yadda shi ma Malam Jibrin Adamu Jibrin Rano, Gwarzon Shekara na 2020, kuma marubucin littafin ‘Dama Sun Faɗa Min’, ya bayyana cewa, “Gasar Gusau ita ce gasar da na fi ƙauna fiye da duk sauran gasannin rubutu da ake sakawa don marubuta, ba don komai ba sai don kasancewa ita ce gasa ɗaya tilo irin ta mai wasu gwala-gwalan damammaki ga marubuta. Na farko dai babban burin kowanne marubuci shi ne ya ga ya buga rubutunsa ya zama littafi, dama ta farko da gasar Gusau take bayarwa ga kowanne marubuci kenan, ta yadda da zarar ya zama gwarzo za a buga labarin nasa a cika masa wannan burin. Ita ce gasar dogon labari kaɗai da ake yi, don haka imma marubuci ya yi nasarar zama zakara ko ya faɗi ta kowanne ɓangare nasara ya samu da zai mallaki cikakken labarin bayar wa ga manazarta masu bibiyar shi. Dama ta biyu kenan da iya gasar ce ke bayarwa. Wani bambancinta da sauran gasannin shi ne ba a keɓance jigo ko a takure tunanin marubuci, ana ba shi dama ne ya shiga duniyar tunaninsa ya yi ta shawagi yana fito da duk abin da yake ransa. Saɓanin yawancin gasanni da ake bayar da jigo.”

Hassana Suleiman Isma’il Matazu, wacce aka fi sani da Sanah S. Matazu, ita ce mace ta farko da ta fara samun nasara a gasar, a shekarar 2021 da littafinta mai suna ‘Fitsarin Faƙo’. Marubuciyar ta ce, “Gasar Tsangayar Gusau ta fi ta BBC Hausa, domin ita gasar Hikayata labari ne gajere kuma kalmomi kaɗan. Idan rabo da sa’a suka yi tasiri wanda bai taɓa cin gasa ba ma zai iya cin Gasar Hikayata. Amma an yi ittifaƙin Gasar Gusau sai jajjirtacen marubuci kuma mai bincike yayin gudanar da rubutunsa, tare da tsantsar hikima ne yake iya haye matakan gasar Gusau.”

Ta ƙara da cewa, “Gasar Gusau sai an tura tsakuren labari na kalmomi 5000, wanda masana sanin abin za su duba su tantance, su ga labaran da suka kamata sannan a saki sakammako.”

Wani abin ƙarin birgewa da wannan gasa shi ne yadda bayan fitar da sakamako, tun kafin a sanar wa duniya ake buga masa littafin da ya samu nasara da shi, a matsayin tsaraba da zai koma gida da ita, kuma ya ajiye don tarihi. Ko kuma ya cigaba da wallafawa yana sayarwa. 

Malam Muhammad Isa Suleiman, mai kula da ɗakin bincike da karatu na Aliyu Mohammed Research Library, da ake yi wa laƙabi da Gusau Institute da ke Kaduna, ya bayyana cewa, akwai ƙa’idoji da dama da alƙalan gasar ke lura da su kafin tantance labari ko karɓarsa a cikin gasar. Daga ciki akwai jigo, taurarin labari, hawa da saukar labari, farko da ƙarshe, amfani da ingantacciyar Hausa, amfani da karin magana, da hikimar warware jigon labari, da zalaƙar harshe wajen riƙe mai karatu. 

Sannan bayan an kammala bin duk waɗannan ƙa’idoji, ana wallafa labarin a matsayin littafi, don a ajiye a ɗakin karatu da bincike na Aliyu Mohammed Gusau, saboda masu zuwa nazari da karatu a ɓangaren adabi da harshen Hausa. 

A cewar Hassana, wacce ita ce shugabar sabuwar ƙungiyar marubuta mata zalla ta Arewa, kuma marubuciyar littattafai da dama. “Gasar Tsangayar Gusau kan fito da martabar marubuci ta hanyar buga masa littafi ko da bai taɓa bugawa ba, saboda suna son duniya ta san wannan marubuci ta kuma fito da ƙimarsa.”

Ko a wannan shekara ta 2024 ma irin waɗannan ƙa’idoji aka duba, kuma cikin izinin Ubangiji, aka fitar da gwaraza uku daga cikin marubuta 120 da suka shiga gasar. Na farko shi ne Rufa’i Abubakar Adam daga Jihar Gombe, wanda ya samu nasara da littafinsa mai suna ‘Marubuciya’. Sai, Ummi Abba Muhammad daga Jihar Borno da ta samu nasarar zama Gwarzuwa ta Biyu da littafinta mai suna ‘Abinda Ka Shuka’. Sai Gwarzuwa ta Uku, Zainab Abdullahi daga Jihar Katsina, da ta samu nasara da littafinta mai suna ‘Wasa Da Rayuwa’.

“Sakamakon Gasar Gusau ta bana ya zo da abin mamaki, inda gwarazan suka fito daga jihohin da ba a cika jin amonsu a gasannin marubuta ba, kamar misalin Jihohin Borno da Gombe,” cewar marubuciya Ummi Abba Muhammad. 

Gwarzon Gasar Tsangayar Gusau, Rufa’i Abubakar da ya samu shiga gasar sau biyu cewa ya yi, “Ban taɓa tunanin zan iya zama marubuci ba, kuma ban taɓa tsammanin zama Gwarzon Shekara ba!”

Ita ma Ummi Abba Muhammad da ta shiga gasar sau uku, a tsorace ta shiga, tana ganin ba irin ta ne za su yi nasara ba. Kamar yadda ta ce, “Ban taɓa sa rai da samun nasara ba, duba da irin manyan marubutan da suka samu gogewa ke shiga gasar…Gasa ce da ake yin ta da kyakkyawan tsari da inganci, duk wanda ka ga labarinsa ya yi nasara to, ya cancanta ne!”

“Lokacin da aka fitar da sakamakon zagaye na ƙarshe na gasar, Zainab Abdullahi da aka fi sani da Lailat, ta kasa yarda cewa labarinta ‘Wasa Da Rayuwa’ shi ne ya shiga cikin fitattun labarai uku na ƙarshe. ‘Na daɗe ina tantamar anya labarin nawa ne kuwa, ko dai gizo ne? Har sai daga ƙarshe na yarda, ina daga cikin waɗanda Allah Ya so kuma Ya nufa da nasara.”

Littafin, ‘Marubuciya’, yana ɗauke ne da labarin wata shahararriyar marubuciyar littatafan Hausa da aka kashe a wani dare. A yayin da jami’an tsaro suke tsaka da bincike ne suka fahimci ashe marubuciyar ta bar wasu adanannun alamomi da idan aka bi su sau da ƙafa za a iya gano wanda ya kashe ta, gami da bayyana musu wani ɓoyayyen sirri na rayuwarta. Kasancewar an riga da an yi jana’izar Adabin Kasuwar Kano ya sa jami’an tsaro shan wahala kafin su kai ga samo littafin. Sai daga ƙarshe bayan sun karanta littafin ne suka yi nasarar gano bakin zaren.

Shi kuwa littafin da ya zo a matsayin na biyu, ‘Abinda Ka Shuka’, labari ne na wani likita wanda ya yi amfani da rigar likitancinsa yake cinikayyar rayukan ‘yan’adam a maimakon ya kasance mai inganta lafiyar su kamar yadda ake tsammani ga kowanne likita. Dakta Tafida ya ɗauki kuɗi a matsayin linzamin sarrafa rayuwarsa gabaɗaya, in dai zai samu kuɗi masu gidan rana duk munin aiki zai iya aikatawa. Ya samu kuɗaɗe da yawa, kuma duniya ta cicciɓa shi ta ɗora shi a saman sararin samaniyar gajimaren jindaɗi. Yana tsaka da fantamawa a cikin daular ne sai kwatsam ta wulwulashi ta kwaɗa ƙeyarsa da ƙasa. Lokaci guda duniya ta yi masa atishawar tsaki. Tun ba a je ko’ina ba ya fara figar kazar wahalar da ya yankawa kansa. 

 ‘Wasa Da Rayuwa’ shi ne littafin da ya samu zama na uku. Kuma labari ne akan wata matashiyar budurwa mai suna Fatima Bintu, wacce ta rayu a wani gari ɗankurna, da Allah Ya albakace shi da tarin albarkatun ƙasar noma. Sai dai kash, duhun jahilcin da mutanen ƙauyen ke ciki a fagen addini da na boko, ya haifar da mummunan giɓi da ya hana garin cigaba. Babu makaranta, haka kuma babu asibiti sai sun yi tafiya mai nisa kafin su kai ga wajen da za a kula da marassa lafiya. Wannan ya haifar da mutuwar mutane da dama ciki har da mahaifiyar Bintu, wacce ta fita Zakka a garin, saboda ilimin da ta samu, duk da ƙalubalen da ta yi ta fuskanta. Matsalar tsaro da ta kunno kai a yankin ita ta yi awon gaba da zaman lafiyar da jama’a ke mora. Yayin da masu garkuwa da mutane ke ɗauki ɗai-ɗai kan mutanen ƙauyen, a lokacin ne Bintu ta shiga nemawa jama’ar ƙauyenta mafita.

Kai daga jin salon waɗannan fitattun littattafai, lallai ka san marubutan labaran ba ƙaramin ɓata hankalin dare suka yi ba, domin samar da labarai masu ma’ana da za su zama hannunka mai sanda ga al’umma. Kuma babu shakka alƙalan sun yi ƙoƙari wajen zaƙulo su.

Kamar yadda yake a manufar wannan gasa, a cewar shugaban ɗakin bincike da karatu na Aliyu Mohammed Research Library Kaduna, Malam Muhammad Isa Suleiman, a ƙarfafa wa marubutan adabin Hausa gwiwa, saboda yadda harshen ke samun koma baya a wajen rubutu da magana, da yadda ake taskance harshe don manazarta da masu tasowa ýan baya. Don haka samar da labarai masu matuƙar inganci da aka yi zuzzurfan bincike akan su, abu ne da yake buƙatar aiki tuƙuru. Ba ga su marubutan kaɗai ba, har ma da masu aikin alƙalancin.

Malam Jibrin Adamu Rano da ya taɓa zama ɗaya daga cikin alƙalan gasar ya ƙara tabbatar da cewa, “Babu wani abu na son rai balle nuna sani ko sabo a cikinta. Duk wanda ya yi nasara to, rabo da cancanta ne suka kai shi matakin.”

A cewar Sanah S. Matazu, an samar da Gasar Gusau ne domin tabbatar da kawo cigaban rubutu da marubuta ta fuskar kawo wata gasa da za ta sa gogayya a tsakanin marubutan adabin Hausa, domin bayyana baiwar da kowanne marubuci yake da ita a fagen rubutu.

Bayan yabo da jinjina da Gasar Gusau da masu shirya ta ke sha daga marubuta da manazarta, akwai wasu hasashe da shawarwari da gwarazan gasar su ma suka bayar, da nufin ƙara bunƙasa gasar nan gaba. Rufa’i Abubakar Adam, Gwarzon Shekarar 2024, cewa ya yi. “Idan zan ba su shawara ba ta wuce ta a ɗan riƙa bai wa sauran marubuta goma da labarinsu ya je matakin ƙarshe ladan alƙalami komai ƙanƙancinsa ba, duk da ana ba su satifiket. Domin su ma sun sha wahala wajen rubuta cikakken labari kamar yadda sauran gwarazan suka sha. Duk da cewa an taimake su ne da aka sa suka rubuta cikakken labari cikin wani ƙayyadajjen wa’adi, wanda inda ba don gasar ba sai mutum ya ɗau shekara da shekaru bai kammala rubutun ba.”

Shawararsa ta zo ɗaya da ta Gwarzuwa ta Uku, Zainab Abdullahi, wacce ta ke cewa. “Ina ganin da za a riƙa duba waɗanda labaran su suka tsallake matakin farko a ba su kyautar kuɗin alƙalami ko babu yawa, da an ƙara musu ƙwarin gwiwa.” Kamar yadda Hassana ma take gani a nata ra’ayin, “Idan zai yiwu ko da dubu 5 ne a riƙa bai wa waɗanda labaransu suka ƙetare matakin kusa da na ƙarshe, wato sauran marubuta 10 daga cikin 13 da aka nemi su kammala cika labaransu.”

A cewar Rufa’i, “Lallai masu shirya wannan gasa sun cancanci a yaba musu, musamman idan aka yi la’akari da yadda mutum ɗaya ne tilo yake ɗaukar nauyin gasar a kowacce shekara ba tare da an samu fashi ba.” Haka ma Hassana ta ce, “Tun daga 2018 zuwa 2024 mutum ɗaya ne yake ɗawainiya da wannan gasa!” 

A ɓangaren masu shirya wannan gasa dai fatansu shi ne, duk marubucin da yake da sha’awar shiga wannan gasa to, ya kiyaye. “Kowa ya yi amfani da basirarsa da fasaharsa, banda satar fasaha. Kar ka ba wani ya yi maka rubutu ka shiga gasa da shi. Kowa ya baje kolin fasaharsa da iliminsa. Wannan shi ne zai tantance ƙarfi da kuma tasirin rubutun mutum. Gasa ce da ake yi a tsaftace tare da tsauraran ƙa’idoji, don kiyaye duk wani abu da zai kawo zargi ko rashin gaskiya da son zuciya.”

Tsohon Ministan Tsaron Nijeriya Janar Aliyu Mohammed Gusau shi ne ya ƙirkiro da Cibiyar Nazari da Bincike ta Gusau Institute da ke Kaduna, kuma shi ne yake ɗaukar nauyin wannan gasa ta marubuta adabin Hausa.

By ukarofi