DAGA MUKHTAR YAKUBU
A ranar alhamis 26 ga Disamba ne aka yi taron bikin ranar Jammaje wato ‘Jammaje Day’ wanda aka saba gudanar da shi a duk ƙarshen shekara.
Taron na ƙarshen shekara ta 2024 wanda aka gudanar da shi a babban ɗakin taro na Musa Abdullahi da ke sabuwar Jami’ar Bayero a Kano, ya samu halartar jama’a daga sassa daban daban na faɗin ƙasar nan.
Tun da farko da yake jawabin maraba da baƙi, Malam Kabiru Musa Jammaje, ya nuna farin cikin sa a game da yadda ya ga taron bikin na shekarar 2024 ya yi tasiri fiye da waɗanda aka yi a baya, saboda yadda jama’ar da suka halarci taron sun wuce duk na tarukan da aka yi a baya. Kamar yadda yake cewa,
“Taron na bana ya yi matuƙar burge ni saboda dumban jama’ar da suka halarta, fiye da na baya. Muna yi wa jama’a barka da zuwa da fatan za a yi taro lafiya a tashi lafiya.”
Ya ƙara da cewa, “Babbar manufar shirya wannan taron shi ne samar da wani dandamali na sada zumunta a tsakanin ɗalibai da suke rassan makarantar Jammaje Academy da da ke garuruwa daban-daban a cikin ƙasar nan, don haka muka tsara duk ƙarshen shekara za mu rinƙa yin taro don a haɗu a ga juna a yi zumunci tare da fahimtar juna.
To a wannan shekarar ma ga shi Allah ya ƙara haɗa mu, cikin farin ciki da begen juna, don haka muna fatan wannan ‘yan uwanta ta zama ta haɗa kan jama’ar wannan kasa domin yin aiki tare cikin fahimtar juna. Allah muna godiya a gare ka bisa ni’imomin ka, kuma muna roƙon ka ka bamu nasara da zaman lafiya a ƙasar mu.”
Shi kuwa a nasa jawabin Farfesa Abdallah Uba Adamu, ya yaba wa Makarantar Jammaje Academy ne saboda ƙoƙarin ta na samar da ilimin Turanci a tsakanin matasan mu na wannan lokacin, wanda ta dalilin wannan makarantar matasa masu yawan gaske sun zama masu ilimi suna koyarwa, wasu kuma sun zama manyan ma’aikata da masu gudanar da harkar kasuwanci cikin ilimi ba tare da yin Turanci ba a duk inda suka samu kansu a duniya.
Ya ci gaba da cewa “Wannan ƙoƙarin na Kabiru Musa Jammaje abin a yaba ne domin ba a koyar da turanci a aji kaɗai ba ya tsaya, domin ya shirya finafinai masu yawa da harshen turanci wanda yake ƙunshe da al’adu na ƙasar Hausa duk a cikin harshen turanci. Hakan ya bada damar yaɗa al’adun Hausa a ƙasashen duniya da kuma koyar da Turanci. Domin idan aka kalli Kabiru Musa Jammaje baya ga koyar da Turanci da yake yi a aji ya kuma rubuta littattafai da dama na koyar da turanci ga finafinai wanda za a iya cewa babu wanda ya bayar da irin wannan gudunmawar a wannan lokacin, don haka sai dai a kamanta Kabiru Musa Jammaje da Abubakar Imam, saboda dumbun gudunmawar da ya bayar.”
Shi ma da yake nasa jawabi, Dakta Bala Muhammad ya bayyana Kabiru Musa Jammaje a matsayin jarumin matashin da ya taimaki rayuwar sa da ta matasa a wannan lokacin da ake buƙatar ilimin Turanci ga matasa.
Ya ce ” Ba ƙaramar baiwa ba ce a samu matasa irin su Kabiru Musa Jammaje a cikin al’umma domin suna da muhimmanci sosai kamar yadda muke gani a yanzu.”
Ya ci gaba da cewa ” Muna buƙatar ilimin Turanci ta kowanne ɓangare na rayuwar matasan mu, amma a yanzu irin tsayuwar da Kabiru Musa Jammaje ya yi, mun samu hanyar cike giɓin don koyar da jama’a ilimi a yanzu ba kamar baiwa ba ce kamar ya tsaya har ya kai ga samar da masu ilimin da su ma suka buɗe makarantun koyar da Turanci lallai muna alfahari da wannan. Kuma na san shi ɗalibina ne a jami’a, mutum ne mai kwazo da son ci gaban jama’a, muna fatan Allah ya linka mana irin su a cikin wannan al’umma tamu.”
Shi ma Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano Abba El-Mustapha ya nuna farin cikin sa da ƙasancewar sa a cikin mahalarta taron, domin a cewar sa ” Kabiru Musa Jammaje mutumina ne, kuma ni na yi masa hanyar shiga harkar fim, har ta kai ga shi manyan malamai suna alfahari da irin gudunmawar da ya bayar a cikin masana’antar Kannywood, to wannan abin alfahari ne a gare ni . Muna Godiya ga wannan abin alheri da Kabiru Musa Jammaje ya yi.”
Bayan manyan baƙi sun kammala jawaban su sai kuma aka kalli fim ɗin ‘Nanjala’ wanda Kamfanin Jammaje Production ya shirya kuma ya ɗauki nauyin shiryawa.
Fim ɗin an ɗauki tsawon sa’a ɗaya da rabi ana kallon sa inda kuma bayan an kammala masu kallo suka faɗi ra’ayoyin su a game da yadda suka kalli fim ɗin tare da bayar da shawarwari.
Bayan kallon fim ɗin kuma mawaƙa sun bajekolin fasahar su in da farko Mudassir Kasim da Maryam A Baba suka yi waƙoƙi na tsawon sa’o’i biyu.
A waƙoƙin da suka yi dai an tuno da waƙoƙin baya kamar shekaru kusan ashirin da suka gabata, tun lokacin da Mudassir Kasim yana tashen waƙarsa.
Haka shi ma Ballo Ibrahim Billy o ya gabatar da nasa waƙoƙin. Sai mawaƙi Abdurrahman Alfazazi shi ma ya gabatar da nasa waƙoƙin.
Fitaccen Mawaƙi Abubakar Sani shi ma ya gabatar da waƙoƙin. Sai kuma Jarumi Abdullahi Adam wato Abale ya nishadantar da mahalarta taron da irin salon maganar sa ta dabanci da yake yi a cikin finafinan.
An dai shafe tsawon wuni guda ana gudanar da taron cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. ‘Yan fim da dama sun halarci wajen taron. Kaɗan daga cikin jaruman da suka halarta sun haɗa da; Falalu Dorayi, Teema Yola, Fatima U S, Nuhu Abdullahi, Surayya Aminu, Rayya ta ‘Kwana Casa’in’ da dai sauran su.
