Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wani jigo a jam’iyyar PDP kuma tsohon mamba a kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Atiku Abubakar a zaɓen 2023, Dr Adetokunbo Pearse, ya buƙaci jam’iyyar da ta tabbatar da ta fidda ɗan takara daga yankin Kudu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Pearse, shi ne shugaba kuma daraktan tattara bayanai da ba da rahoto na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Atiku Abubakar a jihar Legas wanda ya ba da shawarar a yayin wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai ta ƙasa (NAN) a ranar Lahadi a jihar Legas.
Ya ce fidda ɗan takara ɗan Arewa ba lallai ne ya haifar wa da jam’iyyar ɗa mai ido ba a zaɓe mai zuwa na 2027.
“Muna buƙatar wani ne daga Kudancin ƙasar nan domin ƙara shekaru huɗun da ya rage wa yankin Kudu na shekaru 8 ɗinsu na mulki domin mu ceto Najeriya.”
“Wannan ne abin da ‘yan Nijeriya ke buƙata. Don haka, ina bayan wannan tunani da tsari kan cewa bai kamata mu goyi bayan kowanne irin ɗan takara daga Arewa ba,” inji Pearse.
Sannan ya ce jam’iyyarsu ta PDP ba ta buƙatar kowanne irin maja da wata jam’iyya domin cin zaɓe. Wannna ta sa ya yi watsi da zargin yuwuwar yin maja’a tsakanin jam’iyyar Labour da NNPP da PDP domin murƙushe APC a 2027.
“Ina ga da wahala ne jam’iyyar PDP za ta yi maja da wata jam’iyya a 2027.”
A ganinsa jam’iyyun Labour da NNPP ba wani abin a-zo-gani da za su taɓuka ba domin dukkan jam’iyyun gwamna ɗaiɗai suka iya kawowa a babban zaɓen da ya gabata.
Pearse ya ce jam’iyyar PDP za ta lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027 saboda tana da ‘yan majalisa sama da 40 da gwamnoni 12, idan aka tsayar da ɗan yakin Kudu takara.
“Akwai buƙatar mu tattaro ƙarfinmu, mu kai ziyara ga waɗanda suka fice daga jam’iyyarmu.”
“Ko da kaso 60 ne suka dawo jam’iyyar, to lallai fa za mu ci zaɓe mai zuwa.”
“Abin da kawai jam’iyyarmu za ta yi shi ne dawo da shuagabannin jam’iyyarta da kuma muna yin dukkan mai yuwuwa wajen dawo su da matasanmu waɗanda ke jam’iyyar Labour.
Sannan ya alaƙanta rashin nasarar jam’iyyar a zaɓen 2023 da matsalar rarrabuwar kai wajen rabe-raben shiyyoyin ƙasar nan.
“Yawanci muna zaɓen shugaban jam’iyya ne kafin babban zaɓe na ƙasa, saboda haka muna sa-ran shugaban jam’iyyar Dr Iyorchia Ayu zai yi murabus matuƙar dai ba a fidda ɗan Arewa ba a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa.”
