Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano
Ganin yadda ƙungiyar Tallafa wa Marayu da Gajiyayyu ta Gandun Albasa da ke Jihar Kano ta tallafa wa dubban marayu ta fuskoki daban-daban cikin shakaru 22, wanda Alhaji Lawan Dogo ke jagoranta abin a yaba ne kuma akwai buƙatar ƙungiyoyi da jama’a na ko ina su yi koyi da hakan.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Dagacin Gandun Albasa Eng Yakubu Alhassan, a lokacin da yake jawabi wajen taron ƙungiyar da ta saba yi duk shekara domin bayyana abubuwan da take yi ga marayun yankin Gandun Albasa.
Dagacin, wanda ya ce abin sha’awa shi ne yadda idan aka samu wani mutum ya kwanta dama a wannan unguwa abu na farko ƙungiyar kan je gidan ta bada tallafin abinci aƙalla buhun shinkafa da dubu 10 kuma ta cigaba da ɗaukar nauyin yara da mamacin ya bari, wannan alkairi ne babba kuma akwai buƙatar a cigaba da taimakawa marayu dagajiyayyu a ko ina.
Shi ma shugaban ƙungiyar, Alhaji Lawan Dogo, ya ce tun farkon kafa ƙungiyar a shekarar 2002 suka samu haɗin kan iyayen ƙasa da ma’aikatan gwamnati da kuma yan kasuwa da sauran shugabanin al’umma irinsu Marigayi Alhaji Bashir Tofa, wanda a karon farko ya ba ƙungiyar Naira Dubu 150,000 ya kuma ce in dai aikin za su yi to zai cigaba haka, kuma aka yi wanda wannan ce ta bada dama manya suka yadda da ƙungiyar kuma suka cigaba da tallafa mata har zuwa wannan lokaci wanda wannan janye talafun man fetur a 2023 ya jefa ƙungiyar cikin wani hali kamar yadda jama’a suka samu kansu a wannan shekara, inda kuma suke da marayu sama da 800 da ake tallafawa ta fuskar abunci ilimi lafiya da sauransu don haka muna buƙatar taimako daga ko ina.
A ƙarshe, manyan baƙi da dama ne suka halaci wannan taro da kuma gabatar da jawabunsu na jan halakalin muhinmancin mabuƙata kaɗan daga ciki akwai limamin Sera da ke Gandun Albasa Malam Abdullahi, sai Honarabul Yusuf Ado Kibiya, da kuma Wamban ƙareye, da dai sauransu.
