Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Kwamishinan cikin gida da tsaro a Jihar Katsina Dakta Nasiru Mu’azu Ɗanmusa ya jinjina wa jami’an tsaro a jihar bisa ƙoƙarin da suka samu na kashe ‘yan bindiga da lalata sansanin su.
Haɗin gwiwa na jami’an sojoji, ‘yan sanda, DSS, jami’an tsaron al’umma (CWC) da ‘yan banga ne suka gudanar da wannan farmaki.
Sun sami nasarar kashe ‘yan bindiga da raunana da dama da lalata sansanin su a ƙauyukan Ka’idoji,Matso- Matso,Baga, Dogon Marke da Takarda a ƙaramar hukumar Jibiya.
Kwanan baya waɗannan sansanin na yan bindiga da wasu irin su a ƙananan hukumomin Batsari da Ɓatagarawa sun kawo ƙaruwan ta’adanci a wasu sassan jihar.
Da wannan nasara da haɗin gwiwa na jami’an tsaro suka samu na lalata waɗannan sansani a yanzu, ta’adanci ya kusa zama tarihi a waɗannan yankuna.
Kwamishinan ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa gwamnatin Dikko Raɗɗa a tsaye take wajen yin duk abinda zata iya yi wajen kawo ƙarshen ta’addan ci a jihar.
Dakta Ɗanmusa ya yi kira ga al’ummar jihar musamman yankunan da suke fama da rashin tsaro da su baiwa jami’an tsaro goyon baya ta hanyar basu sahihin bayanai kan maɓoyan ‘yan ta’adda a jihar.
