Abin da ya sa na dawo da buga tsofaffin littattafaina – Bala Anas Babinlata

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Ga duk wanda ya yi tashen karatun littattafan Hausa a tsakanin shekarun 1991 zuwa 2000, ba zai kasa sanin wane ne Bala Anas Babinlata ba. Shi ne fitaccen marubucin nan da ya yi tashe a waɗannan shekaru, sakamakon irin littattafan da yake rubutawa masu cike da basira da ɗimbin hikima. Littafinsa na ‘ɗa Ko Jika?’ na daga cikin ayyukansa da suka ƙara masa ɗaukaka da shuhura a duniyar adabi, saboda irin salon rubutun sa mai tafiya da tunanin mai karatu.

A tsakin shekarun da wannan haziƙin marubuci ya yi yana jan zarensa a fagen shahara, Babinlata ya rubuta littattafai fiye da goma, waɗanda akasarin su sun shiga gidaje da dama a ƙasar nan har da ƙasashen waje, wasu kuma an karanta su a tashoshin rediyo daban-daban. Tun a shekarar 2004 bayan da ya fitar da littafinsa na ƙarshe mai suna ‘Mubarak’, marubucin bai sake fitar da wani littafi ba, sai kwatsam a shekarar 2020 ya fitar da wani sabon littafi mai suna ‘Rubutun Fim’, wanda ba na labari ba ne, littafi ne da a ciki ya koyar da dabarun yadda ake rubuta labarin fim. 

Ashe dama duk wannan tsawon lokacin, Bala Anas ya kasance marubucin finafinai ne, mai shiryawa da ba da umarni. Harkar da ya jima a cikinta, tun ma kafin ya fara buga littattafan adabin Hausa. A tattaunawar da muka yi da shi, gwarzon marubucin ya bayyana min abin da ya sa ya dakatar da buga littattafan da yake rubutawa, daga ciki akwai rashin samun isasshen lokacin rubutu, lalacewar harkar kasuwancin littattafan, da ƙarancin shauƙin karatun littafi na wallafa a zukatan matasa, saboda yaɗuwar rubuce-rubucen onlayin da ake fitarwa a baya babu kan gado. 

Shekaru biyar bayan tsawon shirun da ya yi ba tare da ganin sabon bugaggen littafinsa a kasuwa ba, sai dai a sabbin manhajojin sayar da littattafai na onlayin irinsu Okadabooks, ArewaBooks, da kuma Hikaya, Babinlata ya sake wani sabon yunƙuri, domin dawo da tsofaffin littattafansa da suka fara ɓacewa, don masoyansa da masu sha’awar karanta littattafansa su samu damar sake bitarsu, kamar yadda suka daɗe suna ta nema. 

A cewarsa, ya yanke shawarar dawo da buga littattafan ne domin share hawayen masu karatu da suka daɗe suna neman a fitar musu da littattafan da suke kewar sake karantawa.

“Na dawo da buga littattafaina ne saboda tsawon lokaci da makaranta suka ɗauka suna ta bibiyata suna neman littattafan. Tun kafin ɓullar annobar Korona na yi tunanin samar da hanyar da littattafan za su samu cikin sauƙi, amma ba a dace ba. A baya-baya ɗin nan akwai lokacin da Hajiya Hafsat Abdulwaheed, marubuciyar littafin ‘So Aljannar Duniya’, ta kira ni a waya ta ce tana son kwafin duk littattafaina. Na ce da ita, ‘Mama, a yi haƙuri, littattafan nan ba za su bugu ba saboda tsadar kayan ɗab’i.’

“Ba ta haƙura ba. Kwanakin baya da muka haɗu a taron baje-kolin littattafai ta ‘Festiɓal of Authors’ da aka yi a Kaduna sai da ta sake taso da maganar, da wasu makaranta da dama a wajen taron. Saboda haka wannan ya sanya dole na sake komawa na yi tunanin tun da makaranta har yanzu suna buƙatar bugaggun littattafan yana da muhimmanci a samo hanyar da za a iya buga musu. Wannan ne ya sanya na yi tunanin samar da littattafan a matsayin bugu na musamman, ga duk wanda yake da bukata…”

Kawo yanzu dai an fara buga tsofaffin littattafan Bala Anas Babinlata, waɗanda suka kai goma sha ɗaya. A cikinsu akwai, ‘In Da Alƙawari’, ‘Baƙar Ashana’, ‘ɗa Ko Jika?’ ‘Rashin Sani’, ‘Sara Da Sassaƙa’, ‘ƙwarya Ta Gari’, ‘An Yanka Ta Tashi’, ‘Sihirtacce’, ‘Mubarak’, ‘Kulu’, da kuma ‘Ma Ji Ma Gani’. 

Yayin da aka haɗe duk littafi mai na ɗaya da na biyu, zuwa littafi ɗaya dunƙulalle akan farashi naira 2000 kowanne ɗaya, a manhajar ArewaBooks ana sayen littafin ne a naira 500. Amma duk da haka bambancin farashin bai sa masu karatu sun karaya ba, ana cigaba da samun masu buƙatar sayen bugaggun littattafan. Saboda har yanzu akwai mutanen da sun fi son karatu a bugaggen littafi, ba a waya ko kwamfiyuta ba. 

Sai dai ko shi ma Babinlata na da wani saƙo ga waɗanda suka fara sayen sabbin littattafan da aka sake bugawa. Kamar yadda yake cewa, “An gano wasu daga cikin littattafan da ake bugawa suna da matsalar rashin wasu shafuka, kamar misalin littafin ‘ɗa Ko Jika?’ An samu kimanin babi wajen biyar da babu su, ko kuma an maimaita wasu babin a maimakon ainihin wasu. A saboda haka na sake nemo asalin littafin na ɗauko inda babu na yi hotonsa, wanda a halin yanzu duk wanda ya sayi na baya da yake da matsala akwai buƙatar ya dawo da shi a gyara.”

Babu shakka sake dawowar littattafan tsofaffin marubuta irin su Bala Anas Babinlata, babban cigaba ne, kuma hakan zai ƙara ƙarfafa gwiwar sauran marubuta irinsa su sake dawowa fagen ɗab’i, domin fitar da wani sabon tsari na kasuwancin littattafan Hausa. Yayin da masu buƙatar littattafai ta onlayin su ma za su cigaba da cin kasuwarsu ta bayan fage. Kadaran Kadahan, ba kare bin damo!

By ukarofi