Daga BELLO A. BABAJI
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bada umarnin a zurfafa bincike game da harin da ƴan ta’adda suka kai a sansanin sojoji dake Sabon Gida a ƙaramar hukumar Damboa ta Jihar Borno wanda ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji shida.
Harin, wanda aka ƙaddamar a ranar 4 ga watan Junairu ya tada hankalin al’umma tare da sabonta kula da ɗaukar matakan magance matsalolin rashin tsaro a yankin.
Cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labaran Shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar, Shugaba Tinubu ya miƙa gaisuwar ta’aziyyarsa ga iyalan sojojin da suka rasa rayukan nasu, yana mai cewa za a riƙa tunawa da su bisa namijin ƙoƙarinsu wajen kare ƙasa da al’ummarta.
Shugaban ƙasar ya kuma yaba wa sojoji musamman tawagar waɗanda suka yi ruwan wuta ga ƴan ta’addar a lokacin da suke ƙoƙarin kare harin wanda ya yi sanadiyyar hallaka mayaƙan ƴan ta’addar da dama inda ya ce hakan ya nuna yadda sojoji ke zama a shirin ko-ta-kwana.
Ya kuma umarci sojojin da su faɗaɗa ayyukan nasu wajen kai farmaki wa ƴan ta’addar a sansanoninsu haka ma a yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya inda nan ma ƴan ta’adda suke addabar mutanen ƙauyuka.
Har’ilayau, Shugaba Tinubu ya yi kira ga al’umma da ƴan jaridu da su bai wa sojoji goyon baya a ƙoƙarinsu na tabbatar da tsaro a ƙasar.
Kazalika, ya ce gwamnati za ta cigaba da ƙoƙarin kawo ƙarshen ta’addanci da tabbatar da tsaro ga ƙasar da al’ummarta.
