Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Jami’in yaɗa labarai na rundunar ƴan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya tabbatar da afkuwar lamarin.
Ya bayyana cewa su waɗannan jami’an tsaro sun rasa rayukansu a ƙauyen Ɓaure da ke ƙaramar hukumar Batsari bayan sun je ta’aziyar mutuwar wasu mutane.
Da dama sun sami raunuka daga hare haren ƴan bindiga a ƙauyen da harin ya faru.
DSP Abubakar Sadiq ya ce yanzu haka jami’an ‘yan sanda sun shiga ƙauyen Bature da sauran ƙauyukan domin zaƙulo ƴan ta’addan da suka aikata wannan ɓarna
Babu dai wani ƙarin bayani dangane da halin da ake ciki a ƙauyen.
