Daga USMAN KAROFI
A ranar Juma’a, Kotun ɗaukaka Ƙara dake Abuja ta yi watsi da hukuncin babbar Kotun tarayya reshen Kano da ya shafi naɗin sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II. A cikin ƙarar da gwamnatin jihar Kano ta ɗaukaka kan batun sarauta, Kotun ɗaukaka Ƙara ta soke hukuncin kotun ƙasa wanda ya tambayi sahihancin naɗin Sanusi.
Shugaban kwamitin alƙalai uku, mai Shari’a Mohammed Mustapha, ya bayyana cewa babbar Kotun tarayya ta yi kuskuren shiga hurumin da ba nata ba wajen yanke hukuncin kan batun da ya shafi sarauta.
Tun farko, mai shari’a Abdullahi Liman na babbar kotun tarayya reshen Kano ya soke naɗin Sanusi bayan Aminu Babba Ɗan’Agundi ya gabatar da ƙara kan tauye masa haƙƙi, inda ya nemi soke naɗin Sanusi tare da dawo da Bayero. Sai dai Kotun ɗaukaka Ƙara ta bayyana cewa kotun tarayya ba ta da hurumin shiga al’amuran da suka shafi sarauta.
Kotun ta kuma yi watsi da wani hukunci na mai shari’a Amina Adamu Aliyu na babbar kotun Jihar Kano wanda ya goyi bayan dokar soke masarautun da ta sauke Bayero da sauran sarakuna huɗu, tare da tabbatar da naɗin Sanusi a matsayin Sarkin Kano na 16. Kotun ta umarci babban alƙalin Jihar Kano da ya sake tura ƙarar ga wani alƙali don a sake sauraron ta.
Wannan hukunci ya tabbatar da Sanusi II a matsayin sarkin Kano na halal, kamar yadda gwamna Abba Kabir Yusuf ya sake naɗashi a ranar 3 ga Mayu, 2024, bayan rattaɓa hannu kan dokar da ta kafa sabon tsarin masarautun jihar.
