Daga BELLO A. BABAJI
Bayan karaɗe kafafen sadarwa da wani bidiyo da ke nuna yadda wani jami’in ƴan sanda yake wulaƙanta takardun Naira, rundunar hukumar ta sanar da kama shi.
Faifan bidiyon ya nuna yadda jami’in, wanda mataimaki ne na wani ɗan kasuwa mai suna Cif Okoya ya ci mutuncin Naira wanda hakan ya haifar cecekuce acikin al’umma.
A wani rubutu da hukumomin ƴan sanda suka wallafa ta kafar Facebook, sun ce an gano jami’in da ya aikata laifin a lokacin da ƴaƴan ɗan kasuwar suka yaɗa bidiyon da ke nuna yadda lamarin ya faru inda a yanzu haka ya na komarsu domin ya fuskanci hukunci.
Hukumomin sun yi watsi da al’amarin a inda suka bayyana hakan a matsayin rashin ƙwarewa a bakin aiki.
Sun kuma ce za su cigaba da kare martaba da kimar aikin ɗan sanda ta hanyar tabbatar da hukunta duk wanda aka samu da laifi.
