‘Yan bindiga sun kai hari asibiti, sun harbe likita da sace ma’aikata a Katsina

Spread the love

‘Yan bindiga sun kai hari babban asibitin da ke ƙaramar hukumar Ƙankara a Jihar Katsina, inda suka harbi wani likita tare da yin garkuwa da wasu ma’aikatan asibitin da ba a san adadinsu ba.

Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:00 na yammacin ranar Talata, inda suka harbi Dr. Murtala Sale Dandashire a ƙafa. Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun shiga harabar asibitin cikin tsari, suna ta harbe-harbe, wanda ya jefa ma’aikata da marasa lafiya cikin firgici. An tabbatar da cewa Dr. Dandashire, wanda aka harba a ƙafarsa, yana raye kuma yana samun kulawa a wani asibiti da ba a bayyana ba.

Dr. Dandashire, wanda ya kammala karatu daga Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) Zariya a Jihar Kaduna, ya samu lambobin yabo guda 13, ciki har da na “ɗalibin da ya fi kowa cin jarabawa” a ajin shekarar 2019. An harbe shi ne a lokacin da yake kula da marasa lafiya da suka je neman magani. Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina, Sadiq Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa suna ci gaba da bincike domin gano cikakken abin da ya faru.

By ukarofi