Ko akwai bambanci tsakanin auren ba ni-in ba ka da kuma auren ‘shigar’ a Muslunce?

Daga AISHA ASAS 

Mai karatu barka da yau, barkanmu da sake kasancewa a shafin Iyali na jarida mai farin jini, Manhaja. 

A yau darasin namu na buƙatar hankalin mai karatu, domin darasi ne da dayawanmu ba mu san da zamansa ba, ko in ce za mu iya kawar da kai idan mun ga an yi shi ba tare da ɗaukarsa a matsayin aibu ba.

Bari mu soma da bayanin bambancin auren ba ni-in ba ka da kuma auren ‘shigar’. Dukkansu suna da ma’ana iri ɗaya ne, sai dai ‘shigar’ a duk inda ya zo yana a matsayin haramun ne, yayin da ɗan da aka faɗa zai iya zama a matsayin haramun kuma zai iya zama halastacce.

Auren shigar wata ɗabi’a ce da mutanen baya ke yi na guje wa biyan sadaki a aurensu, wato idan kana da ‘ya abokinka na da ita shi ma, sai ku yi yarjejeniya kan cewa, ya ba ka ‘yar tasa, kai ma ka ba shi taka, sai ya zama kun ɗauki sadakin da za ku bayar a matsayin na ‘yar da za ku aurar, ma’ana kowane daga cikinku ba zai bayar da sadaki ba, wato kun yi ban gishiri in baka manɗa, ‘trade by barter’ a turance.

Idan mutanen biyu suka yi hakan to wannan auren ya haramta, kuma abinda Musulunci ke ƙoƙarin ƙarfafawa anan haƙƙin mace ga sadakinta. Ba wanda ke da iko da sadaki face wadda za a aura, ba ya halasta ko ga iyaye su ci sadakin ‘yarsu ba tare da amincewarta ba. Shi ya sa aka ce idan an kawo sadakin a hannunta mata su, a ba ta zaɓi kan yadda za ta yi da su domin dukiyar aurenta ce, idan ta yafe wa iyayen ko ma mijin da za ta aura, to za su iya ci hankali kwance. 

Idan mun fahimci zancen da kyau za mu fahimci cewa rashin bayar da sadakin ne kawai ya lalata auren. Amma idan a lokacin da suka yi sha’awar auren ‘ya’yan juna, kowanne daga cikinsu ya kawo sadakin yarinyar da yake son ya aura, an hannunta mata, ba tare da an yi amfani da dukiyar an biya sadakin na ɗayar ba, wato idan an kai wa uban, ya ajiye su a gefe, ya ɗiba daga tasa dukiyar ya biya sadakin ‘yar ta abokin nasa, to wannan babu laifi, kuma halastaccen aure ne aka gudanar. Saɓanin hakan ne kawai zai iya zama haramun. 

Daga ƙarshe, zan yi amfani da wannan dama na yi kira gare mu da mu tashi tsaye, mu ba wa neman ilimin addini muhimmanci, domin da yawan lokuta muna kai kanmu wuta ba tare da sani ba.

Idan na ce sani a nan ba za mu iya kiransa jahilci ba, wanda a wasu lokuta ba a kama mai shi da laifin domin a rashin sani ya yi, wanda hakan zai iya kasancewa ilimin ne bai kai a inda yake ba, saɓanin zamanin da muke ciki a yanzu, da ilimin ke biyar mu har a gadon kwanciyarmu, kenan ba mu da hurumin kafa hujja da jahilci.

Mu tuna, ba ya halasta, aikata wani aiki har sai ka san hukuncin Allah a cikinsa.