Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
A ƙarshe, ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya ta amince da ƙudirin sake fasalin harajin da ake shirin yi a Majalisar Dokokin ƙasar, amma sun gabatar da sabuwar hanyar rabon harajin ɓAT.
Hakan na ƙunshe cikin sanarwar da ƙungiyar gwamnonin ta fitar a ranar Alhamis, wadda ta samu sa hannun shugabanta kuma Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaƙ.
Gwamnonin sun kuma fitar da sabon tsari na rabon haraji a Nijeriya, bayan wata ganawa da suka yi da kwamitin da aka kafa domin nazari kan ƙudurin sabuwar dokar harajin.
Ana iya tuna cewa, a ƙarshen shekarar da ta gabata ce Shugaba Bola Tinubu ya gabatar wa Majalisar Tarayyar ƙasar ƙudurin gyara dokar haraji ta ƙasar, lamarin da ya haifar da zazzafar muhawara da raba kawunan shugabanni a ƙasar.
Wannan ya kai ga cewa Shugaba Tinubu da Majalisar Dokokin Tarayya sun jingine batun muhawara da amincewa da dokar har sai bayan an sake nazari a kanta.
Sai dai a zaman da suka gudanar a Abuja, gwamnonin sun yi gyare-gyare a ƙudurin harajin, musamman ɓangaren rabon harajin cinikayya na VAT, wanda shi ne ya fi janyo cece-ku-ce.
Sabon tsarin rabon harajin ɓAT da gwamnonin suka gabatar ya ƙunshi cewa kashi 50 cikin ɗari za a raba daidai-wa-daida tsakanin dukkanin jihohi.
Haka kuma, gwamnonin sun yi wa ƙudirin gyaran fuska da cewa kashi 30 cikin ɗari za a raba gwargwadon gudumawar da kowace jiha ta bayar wajen tattara harajin
Sai kuma kashi 20 cikin ɗari za a raba gwargwadon yawan al’ummar kowace jiha.
Hakazalika, gwamnonin sun kuma bayar da shawarar cire sashen sabon ƙudurin dokar da ya shata lokacin dakatar da ware wa gidauniyar tallafa wa manyan makarantu da takwarorinta da sabuwar dokar ta ambato kuɗi.
“Mambobin wannan ƙungiya sun amince cewa kada a yi ƙari a harajin VAT, ko rage harajin kamfanoni na CIT a wannan lokaci, domin tabbatar da daidaiton tattalin arziki,” inji sanarwar.
Ta ƙara da cewa, “muna bayar da shawarar kada a sanya wani ɓangare a dokar da zai iyakance kuɗaɗen tafiyar da lamura da ake ware wa TETFUND, NASENI da NITDA.”
A ƙarshe, sanarwar ta ce ƙungiyar gwamnonin tana goyon bayan cewa a yanzu Majalisar Tarayyar za ta iya ci gaba da muhawara kan dokar domin samun amincewa.
