Salon mulki da tsare-tsaren Tinubu za su kai mu tudun mun tsira – Uba Sani

Spread the love

Daga SANI HAMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya ce, Shugaba Tinubu ya shirya tsaf domin sake fasalin Nijeriya da kuma ɗora ta kan gwadaben cigaba mai ɗorewa.

Gwamnan ya ce, idan aka yi la’akari da manufofin shugaban ƙasa da ke cike da ƙarfin guiwa za a ga sun ɗan haifar da ƙalubale da tsanani, amma komai zai wuce, domin tsananin na ɗan wani lokaci ne.

Gwamna Uba Sani ya yi waɗannan kalamai ne a yayin wani taron lakca na kwana ɗaya da Arewa Think Tank ta shirya a ranar Talata inda a cikin jawabinsa na maraba, yake bayyana buƙatar nuna juriya domin cin ribar gyare-gyaren da gwamnatin ke kawowa.

“A gaskiya, mun ma fara kawo sauyi. Tattalin arziƙin ya fara bunƙasa da sauri. Nan ba da daɗewa ba, ‘yan Nijeriya za su fara ganin tasirin sauye-sauyen. Abin da shugaban ƙasa ke buƙata a halin yanzu shi ne goyon baya.”

“Shirin sabunta fatan ‘yan Nijeriya da shugaban ƙasa ya kawo daga irin haken nesansa ya mai da hankali ne wajen mayar da Nijeriya cibiyar zuba jari a duniya.”

“Manufar shirin na fito da – dimokraɗiyya da samar da cigaba da shiga da ‘yan Nijeriya mazauna ƙetare – kishin ƙasa da nuna ƙarfin guiwa.”

A cewar gwamnan, bunƙasa Nijeriya da bai wa ‘yan Nijeriya sabuwar rayuwa abu da ke buƙatar bai wa ɓangaren noma muhimmancin da ya kamata.

Gwamnan ya ce, “A lokacin da aka bai wa Nijeriya ‘yancin kai, noma shi ne babban ginshiƙin tattalin arziƙinta. A dukkan ɓangarori uku na Nijeriya, an dogara ne da noma wajen samar da kayan more rayuwa da gina ɗan’adam.”

Sai dai ya nuna damuwarsa kan yadda samun man fetur ya sa aka yi watsi da noma inda ya nuna buƙatar a dawo a rungumi noma da zuba jari sosai a cikinsa, domin noma na da ƙarfin magance matsalar talauci da rashin aikin yi da matsalar tsaro a Nijeriya.

Gwamnan ya ce, “shugaba Tinubu tuni ya fara wannan ƙoƙari na bai wa noma muhimmanci da zuba jari kan noman zama da tallafa wa ƙananan manoma.”

A cewar gwamna Uba Sani, irin huɓɓasan da shugaba Tinubu ya yi a ɓangaren noma, abu ne da ba a taɓa samun gwamnatin da ta yi irin sa ba a Nijeriya.

“Shugaba Tinubu yana ba wa sauran gwamnatoci tallafin kuɗin da kayan aikin da ya kamata. A kwanakin baya ne shugana ya kafa tarihin samar da ma’aikatar bunƙasa kiwo wacce ake da fatan zata sanya Nijeriya zama jagaba wajen kiwo a nahiyar Afirka, a cewar gwamnan.

A irin nasa ƙoƙarin kuwa, gwamna Uba Sani, ya ce gwamnatinsa ta mai da hankali ne wajen buƙasa yankunan karkara, yana mai cewa, “mun mai da hanakli ne wajen bunƙasa cigaban karkara ta farawa da ƙananan hukumominsu zuwa ga su kansu ƙauyuka domin samun cigaban tattalin arziƙi.”

Ya ce, “ta hanyar noman amfanin gona kamar masara da gyero da waken suya da ya kai sama da tan miliyan 2, jihar Kaduna ta zama jihar da ta fi kowacce noman masara a Nijeriya kuma ɗaya daga cikin masu samar da citta a duniya.”

“Ubangiji ya albarkaci jihar Kaduna da ƙasar noma. Sai dai har yanzu ƙoƙari muke mu ci ribar wannan albarka. Kuma ta hanyar kuɗi da muka ware domin noman rani, musamman ta wajen amfani da kogin da kayan aikin noma na zamani, za mu yi nasarar wajen tallafa wa manomanmu,” a cewarsa.

Gwamnan ya ce, “gwamnatina na zuba jari mai yawa wajen noman zamani da kuma ƙananun kayan aikin gona da ake da su.”

“A kakar noma ta 2024, mun raba motocin takin har 500 inda aka bai wa ƙananun manoma 120,000 kyautar buhun taki kowannensu daga buhunhuna 240,000 da muka fitar. Sannan mun raba kayan aikin gona ga dubbun nan mutane a ƙarƙashin shirin Tallafin Noma (A Koma Noma).”

“Mun rage wa manomanmu halhalun kashe kuɗi wajen sayen kayan aikin gona ne, domin su samu ƙarfin guiwar yin noma yadda ya kamata da cin moriyar albarkar yabanya mai kyau da za su samu.”

Sauran waɗanda suka halarci wurin taron akwai ministan albarkatun ƙasa, Dele Alake, babban mashawarci kan kafafen yaɗa labarai, Sunday Dare, da shugaban taron kuma tsohon babban hafasan tsaron Nijeriya, Martin Luther Agwai. Dukkanninsu haɗi da gwamnan jihar Kaduna sun samu lambar karramawa a wurin taron.

By ukarofi