Gidauniyar haɗin kan Funtua ta yi alƙawarin inganta Ilimi da kiwon lafiya

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Wata gidauniya mai suna ‘Funtua Unity Foundation’ ta sha alwashin haɗa gwiwa da gwamnati da ƙungiyoyi masu zaman kansu da ‘yan kasuwa da kuma sarakunan gargajiya domin samar da ci gaba mai ɗorewa a ƙaramar Hukumar Funtua ta jihar Katsina.

Shugaban gidauniyar, Kwamred Mannir Suleiman, ya bayyana haka a lokacin da ya jagoranci sauran ‘ya’yan ƙungiyar zuwa ziyarar ban girma ga Sarkin Maskan Katsina Hakimin Funtua, Alhaji Sambo Idris Sambo, a fadarsa da ke Funtua.

Kwamared Mannir Suleiman ya ce gidauniyar za ta mayar da hankali ne kan muhimman fannoni guda bakwai da suka haɗa da haɗin kai, da ilimi, da samar da aikin yi, da bunƙasa sana’o’i, da inganta harkar kasuwanci, da sa ido kan jami’an gwamnati, da kuma haɗa gwiwa da ƙungiyoyi don haɓaka tattalin arzikin ƙaramar hukumar Funtua.

Ya ce gidauniyar za ta bunƙasa ilimi da ci gaban rayuwar yara da matasa domin su zamo masu dogaro da kai.

Kwamared Suleiman ya ce har ila yau gidauniyar za ta haɗa hannu da fitattun ’yan asalin garin Funtua wajen samar da guraben aikin yi a matakin jiha da tarayya ga waɗanda suka kammala karatu a manyan makarantu da kuma samar da jarin kasuwanci ga matasa.

Ya shugabannin gidauniyar sun kai ziyarar a fadar Sarkin Maska ne domin naɗa shi a matsayin Urban gidauniyar da kuma neman albarkarsa tare da roƙonsa da ya yi amfani da muƙaminsa wajen ƙarfafa ayyukan gidauniyar.

A nasa jawabin, Hakimin na Funtua, Alhaji Sambo Idris Sambo, ya amince da zama uban gidauniyar, ya kuma yaba da hangen nesan waɗanda suka assasa ta.

Ya bayyana gidauniyar a matsayin abin farin ciki musamman a daidai lokacin da Funtua ke fuskanci ƙalubale da dama na zamantakewa da tattalin arziki.

Ya yi alƙawarin bayar da cikakken goyon baya da haɗin kai ga gidauniyar tare da haɗa kai da shugabanninta domin cimma manufofinta.

By ukarofi