Mambila: Tinubu ya musanta tilasta wa Obasanjo da Buhari bada ba’asi a kotun Faransa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Fadar Shugaban ƙasar Nijeriya ta musanta batun tilasta wa tsofaffin shugabannin ƙasa Muhammadu Buhari da Olusegun Obasanjo bayyana a gaban wata kotun cinikayya ta ƙasa da ƙasa da ke birnin Paris a ƙasar Faransa domin bada bahasi dangane da kwangilar aikin gina cibiyar samar da wutar lantarki ta Mambilla da ke Jihar Taraba. 

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, Bayo Onanuga, a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar dangane da batun, ya ce sam gwamnatinsu ba ta tilasta wa tsoffin shugabannin ƙasar biyu zuwa Paris ba domin bayar da bahasi.

Rahotanni dai sun ta fitowa daga kafafan watsa labaran Nijeriya cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ce ta tilasta wa tsoffin shugabannin zuwa Paris.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “duk da cewar batun shari’ar abu ne da bai kamata a bayyana shi a kafafen watsa labarai ba, amma muna ba ku tabbacin cewa gwamnatin shugaba Tinubu ba ta tilasta wa kowa ba kan ya bayar da shaida ko ya ƙi bayar da shaidar a gaban kotun ba.”

Dukkan mutanen da suka bayyana a kotun sun yi hakan ne bisa raɗin kansu da kuma kishin ƙasa,” inji Bayo Onanuga.

Idan dai ba a manta ba, a 2003 ne gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ta bai wa kamfanin na Sunrise kwangilar gina da kula da tashar wutar lantarki ta Mambilla da za ta samar da megawatt 3,050.

To, sai dai a wata tattaunawa da Olusegun Obasanjo ya yi da jaridar The Cable a 2023, ya ƙalubalanci ministan wutar lantarki na zamaninsa, Olu Agunloye wanda shi ne ya bayar da kwantaragin ga Sunrise.

“A lokacin da nake shugaban ƙasa, babu ministan da yake da damar amince wa da abin da ya zarce naira miliyan 25 ba tare da sahhalewar shugaban ƙasa ba. Ba zai yiwu Agunloye ya bayar da kwangilar dala biliyan shida ba tare da izinina ba kuma ni dai ban ba shi izini ba.”

A watan Okotoban 2017 ne kuma kamfanin na Sunrise ya shigar da ƙarar neman diyyar saɓa ƙa’idar kwantaragin, inda yake neman gwamnatin Nijeriya ta biya shi diyyar dala biliyan biyu da miliyan 354.

Rahotanni sun nuna cewa a 2020 tsohon ministan lantarki na Nijeriya zamanin shugaba Buhari, Sale Mamman ya cimma sulhu da kamfanin a wajen kotu inda aka amince za a bai wa kamfanin dala miliyan 200 a cikin makonni biyu.

To, amma kamfanin ya ɗaukaka ƙaran neman diyyar dala miliyan 400 a kotun cinikayya ta ƙasa da ƙasa da ke Paris bisa zargin karya ƙa’idojin yarjejeniyar kwantaragin.

Kamfanin ya ce ya kai ƙarar ne saboda gwamnati ta karya alƙawarin biyar diyyar dala miliyan 200 a cikin makonni biyu.

By ukarofi